1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Haramta shan shisha a Kano

Nasir Salisu Zango LMJ
February 1, 2022

Al'umma na mayar da martani kan matakin Hukumar Hisba ta Kano da ke Najeriya, na fara kai samamen kamen masu sha da sayar da shiha bayan sanya dokar haramta ta'ammali da ita a fadin jihar.

Nigeria Kano Justiz Hisbah
Hukumar Hisba ta jihar Kano dai, ta saba kama wadanda take ganin sun taka shari'aHoto: Getty Images/AFP/A. Abubakar

Tun da fari dai Hukumar ta Hisba, ta sanya dokar haramta saye da sayar da tabar shishar. Inda ta zargi cewa mafi akasarin masu tu'ammali da shishar da suka kasance matasa, na saka tabar wiwi da sauran kwayoyin da magungunan da ke saka maye aciki kafin su zuka. Sai dai kuma duka da cewa wasu na yaba matakin na Hisba, masana shari'a na ganin cewa matakin nata ya wuce gona da iri. Duk da cewa Hukumar Hisba din ta ayyana sanarawa tare da bayar da umurnin hana tu'ammali da shishar, wasu daga cikin wadanda aka kama din na cewa ba su ma da masaniyar hakan. Koda yake wasu da DW ta zanta da su bayan da hukumar ta kai samame wajen shan shishar ta kuma cafke su, sun nunar da cewa za su daina sha baki daya da zarar sun samu 'yancinsu daga hisba.