Kano ta shiga yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi
December 18, 2013Sakamakon matsayin da jihar Kano ta rike na zama jiha mafi yawan matasa masu shan miyagun kwayoyi, mahukuntan jihar sun tashi haikan domin kawo karshen shaye shaye ga matasan jihar. Yanzu haka dai an kirkiri wata cibiya ta farfado da matasa masu shaye shaye, inda ake koya musu sana'oi, a kuma basu tallafi da nufin dogaro da kai. Yanzu haka dai har an fara yaye matasa 23 daga wannan cibiya, wacce ake ganin samun ta zai taimaka wajen magance shaye shaye a jihar.
Dimbin matasa ne a jihar Kano ke shiga harkar shaye shaye, wannan kuma bama ga maza ba domin suma mata sukan shiga wannan harka, musamman ma a fannin shan kwayoyi da magungunan tari masu sa maye samfurin Parkalin da Benylin da sauransu. Karuwar irin wannan matsala shine yasa jihar ta rike kambin jihar da ta fi kowacce yawan masu shan miyagun kwayoyi a fadin Najeriya, hakan ne ma ya sa gwamnatin jihar ke daukar matakan shawo kan wannan matsala. Cikin matakan kuwa har da kirkirar wata cibiya wacce ake kebe masu shan kwayoyi a ringa basu horo tare da koya musu sana'oi, harma kuma an fara yaye matasa 23 da suka sami horo a wannan cibiya kamar yadda kwamishiniyar harkokin mata da walwalar jama'a Dr Binta Tijjani Jibril ta bayyana.
Wani matashi da ke cikin wadanda wannan cibiya ta yaye ya bayyana cewar hakika shi kam ya yi sallama da shaye shaye, kuma dama ya koya ne daga abokansa, kuma a yanzu babban burinsa shine ya koma makaranta ya cigaba da karatu. Sai dai kuma masu fashin baki na cewar duk da cewar kirkirar cibiyar yayi daidai, to amma tsadar shiga cibiyar zai iya kawo nakasu wajen nasarar da ake bukatar a cimma, kamar yadda Abubakar Muhammad dake fashin baki akan al'amuran yau da kullum ya bayyana.
Sai dai kuma wasu na ganin kamar an yi tuya an mance da albasa wajen kirkirar cibiyar duba da cewar ba a tanadi wurin mata a cikin ta ba, duk da cewar ana kara samun matasa mata masu shaye shaye. Ba wai matasa ne kadai ke shaye shayen ba,domin yanzu haka rundunar yaki da shan miyagun kwayoyi ta jihar kano tat a kama wani tsoho mai kimanin shekaru 92 wanda ake kama shi yana zukar tabar wiwi. Yanzu haka dai an kara diban matasan da za a horar nan gaba a wannan cibiya,domin hade su da wadanda aka horar a yaye su a kuma basu tallafin far asana a domin dogaro da kai.
Mawallafi: Nasiru Salisu Zango
Edita: Umaru Aliyu