1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tawagar Buhari ta sha jifa a jihar Kano

Nasir Salisu Zango LMJ
January 30, 2023

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyarar kaddamar da ayyuka a jihar Kano, ziyarar da aka shawarce shi ya dakatar da ita saboda fargabar abin da ya faru yayin makamanciyarta a jihar Katsina amma ya ce ba fashi.

Najeriya l APC | Muhammadu Buhari | Kano
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Nigeria Prasidential Villa

Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari dai, ya bude cibiyar adana bayanai ta zamani yankin Arewa maso Yammacin kasar a jihar ta Kano. A jawabinsa ministan sadarwa da bunkasa tattalin arziki na zamani Isa Ali Pantami ya bayyana cibiyar da ta kasance ta farko a arewacin Najeriya da cewa, an yi ta da nagartar da babu irinta a fadin duniya ta la'akari da irin kayan aikin da aka zuba mata. Ya kara da cewa, an zabi jihar Kano ne saboda ita ce cibiyar kasuwanci a arewacin Najeriyar. Haka kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya bude wasu hanyoyi da gadoji da kuma sabon ginin Soron Ingila, a fadar Sarkin Kano. A jawabinsa, mai martaba sarkin na Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yabawa Shugaba Buhari a kan sassauci wajen kara wa'adin daina karbar tsofaffin kudi zuwa ranar 10 ga watan gobe.

Kano na zaman guda daga cikin jihohin da Buhari yake da magoya bayaHoto: DW/Y. I. Jargaba

Daga bisani ne kuma Shugaba Buhari ya yi sansani a gidan gwamnatin Kanon, inda a cikin jawabinsa yake cewa 'yan Najeriya saurin mantuwa gare su. Babban abin da ya zama bambarakwai wai namji da suna Hajara dangane da ziyarar shugaban ta wannan lokaci shi ne, yadda aka samu musayar yawu tsakanin magoya bayansa da wasu kusoshin gwamnatin Kano wadanda suke cewar shugaban ya yi zamansa ba sai ya zo ba. Bashir Ahmad guda ne cikin hadiman Shugaba Muhammad Buhari kuma ya ce, babu wani zaman doya da manja tsakanin shugaban kasar da gwamnatin Kano. Sai dai kuma duk da kiraye-kiraye na a kiyayi rashin tarbiya yayin ziyarar shugaban, an samu wasu matasa da suka yi ta jefe-jefen duwatsu ga tawagar shugaban a kan titin Hotoro. Koda aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano kan wannan rashin daraja, sai ya ce jami'ansu da suka je wajen ba su dawo ba balle ya saki bayanin halin da ake ciki.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani