1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

OPEC za ta kara yawan man fetur da take hakowa

Suleiman Babayo ATB
March 2, 2022

Manyan kasashe za su fito da man fetur da suka tanada domin rage radadin da aka shiga bayan kutsen Rasha a Ukraine inda kasashe masu arzikin man fetur ke duba yuwuwar kara man fetur da suke fitarwa kasuwannin duniya.

Logo OPEC
Hoto: Pavlo Gonchar/ZUMAPRESS.com/picture alliance

Shugabannin kasashe masu arzikin man fetur na kungiyar OPEC a wannan Laraba suke duba yuwuwar sanin yawan man fetur da za su fitar kasuwannin duniya sakamakon halin da kasuwar ta shi bayan harin da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine.

Akwai yuwwuar kasashe za su kara kimanin gangar danyen man fetur 400,000 a kan abin da suke fitarwa kowace rana.

Tun daga watan Yulin shekarar da ta gabata kasashen masu arzikin man fetur suke kara yawan man fetur da suke kai wa kasuannin duniya sannu a hankali sakamakon farfadowar lamura a duniya, bayan samun annobar cutar coronavirus da ta janyo rufe harkokin rayuwa a duniya.

Zuwa wannan Laraba farashin gangar danyen man fetur ya kai kimanin dalar Amirka 110, saboda yanayin da aka shiga inda kasar Rasha da ke sahun gaba a masu makamashi ta kaddamar da hare-hare a kan kasar Ukraine.

Tuni kasashen Amirka, Jamus, Faransa, Birtaniya, Japan and Canada suna bayyana shirin sake kimanin gangar mai milyan 60 daga cikin wanda suka ajiye domin rage radadin da za a fuskanta cikin wannan yanayin.