1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Neman amfani da mafarauta kan yaki da Boko Haram

May 14, 2021

Gwamnatin jihar Yobe da ke Najeriya ta fara shirin amfani da mafarauta da ‘yan baka gami da ‘yan banga domin tallafawa Sojojin yaki da Boko Harama dai dai lokacin hare-haren Boko Haram ya tsananta a jihar.

Nord Nigeria Anti Boko Haram Bürgerwehr Vigilante
Hoto: picture-alliance/dpa/Stringer

A ‘yan kwanakin nan mayakan Boko haram sun zafafa hare-hare da su ke kai wa a sassan jihar yobe bayan saukin su da aka samu tsawon lokaci abun da ya ke haifar da fargaba tsakanin al’ummar jihar. Tun bayan harin da bangaren mayakan Boko Haram suka kai hari tare karbe iko da garin Geidam na wasu kwanaki da ma harin da suka kai a kananan hukumomi a jihar Yobe suke fadi tashin nemo hanyoyin magance hare-haren da mayakan ke kai wa. Wannan ne ya sa gwamnatin jihar ta yanke shawara fara amfani da mafarauta da ‘yan baka da ‘yan banga domin taffawa komarin jami’an tsaro ganin su na ilimin ya yankuna da dazukan da mayakan ke boye a ciki.

Karin Bayani:Najeriya: Kame masu bai wa Boko Haram kudi

A wani taro na tsaro na gagagwa da gwamnatin jihar ta gudanar gwamnatin ta yi kira ga sojojin da su bai wa mafarauta da ‘yan banga damar yin aiki da su wajen yaki da Boko Haram kamar yadda ya faru a wasu jihohin. Mafarauta sun ce sun ji dadin wannan yunkuri na gwamnati inda su k ace in har za a samar mu su da kayayyin aiki za a sha mamaki aikin da za su yi na tabbatar da tsaro.

Hoto: Reuters/Joe Penney

A cewar Malam Adamu dan Borno wani mai fashin baki kan harkokin tsaro a Najeriya ya ce lallai jihar Yobe ta yi farar dabara  sai dai ya kamata a saka ido kan wadanda za su yi aikin taya jami’an tsaro saboda gudun yin kitso da kwarkwata.

Akwai dai jihohi da dama da suka yi irin wannan tsarin a baya kuma sun samu nasara.

Ga misalijihar Borno ta jima da aiwatar da wannan tsari kuma sau da yawa an yaba bisa kokarin mafarautan a kokarinsu na taya jami’an tsaro yaki don kawo zaman lafiya. Sai dai Ali Rabkana Gashua Babban Odita na Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa ya ce in har ana son samun nasaar shigar mafarauta da ‘yan baka cikin aikin taya jami’an tsaro yaki to dole a samar mu su da tallafi na yadda za su rike kan su da iyalansu. Masharhanta na ganin koda za a yi amfani da mafarayra da ‘yan banga dole sai sauran al’umma sun ba su hadin kai tare da taimaka mu su da bayanai na sirri ta yadda za su iya yin aiki cikin sauki. Rikicin na Boko Haram ya haifar da 'yan gudun hijira a sassan Najeriya.