Karancin abinci da magunguna a birnin Fallouja
February 2, 2016Talla
Birnin na Fallouja dai da ke a nisan kilomita a kalla 50 a Yammacin birnin Bagadaza, na a hannun 'yan kungiyar IS ne amma kuma sojojin gwamnatin ta Iraki sun yi masa kawanya. A cewar Gwamnan jihar ta Anbar Sohaïb Al-Raoui a halin yanzu dai babu wasu dakaru da kan iya shiga cikin birnin domin kula da shigar da kayan agaji, don haka sai dai a jefo ta sama. Suma dai wasu mazauna birnin na Fallouja da aka tuntuba ta wayar tarho sun ce al'umma na fuskantar babban karancin kayayakin abinci, da magungunna da kuma man fetir na zirga-zirga.