1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Karancin kudin shiga a jihohi

October 30, 2024

Duk da karuwar kudin shigar Tarayya, jihohin Najeriyar da daman gaske na fuskantar karuwar rashin kudin da ke shafar kokarin sauke nauyin al'umma da yake kansu.

Najeriya | Jihohi | Kudin Shiga
Tsadar rayuwa na kamari a NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Wani sabon rahoto dai ya ce jihohi guda hudu ne a cikin Tarayyar Najeriyar ke iya tsaiwa da kafafunsu a halinyanzu, a karkashin wani tsarin da ke dada nuna dogaron jihohin a kan kudin tarayyar ga tafi da harkokin miliyoyin al'ummarsu. Kudin na Abuja dai ne a fadar wani sabonrahoto ke zaman madogarar sauke nauyin kimanin kaso 55 cikin 100 na albashi da ragowar bukatu na yau da na gobe, a wasu jihohin kasar 32. A yayin kuma da a wasu 14, irin wadannan kudi ne ke zaman kaso 70 cikin 100 na damar sauke nauyi. In ban da wasu jihohi guda shida daukacin jihohin Najeriyar sun zubar da damar tara kudin shigar cikin gidan, duk da hukumomin tara harajin da ke a jihohin. A shekarar da ta shude dai jihohi da ke Kudu maso Yammacin kasar ne kadai suka nuna alamun sauyi, tare da tara abun da ya kai Naira triliyan daya da miliyan dubu 200 da sunan harajin cikin gida. Duk da yawan jihohin da ke Arewa maso Yamma dai, yankin ya kare da harajin da bai wuci Naira miliyan dubu 200 ba.

Kano: Neman mafita ga tsadar man fetur

03:06

This browser does not support the video element.

Ita kanta jihar Legas da ke zaman ta kan gaba cikin batun na haraji a daukacin kasar dai, a fadar Abubakar Ali da ke zaman kwarrare ga tattalin arziki ta dauki hankalin al'umma ta jihar kafin shawo kan 'yan kasar su biya harajin. Can cikin karatun dauri dai, jihohi da yawa cikin kasar na iya sauke nauyi da kila tallafawa tarayyar sakamakon kudin shigar da suke samu. Adamu Aliero dai na zaman tsohon gwamnan Kebbi, kuma ya ce harajin cikin gida neman sa ake. Jihar Kaduna na zaman ta kan gaba cikin batun na haraji a daukacin arewacin Najeriyar, inda a bara kadai ta karbi abun da ya kai Naira miliyan dubu 62. Kudin kuma da a cewar gwamnan  jihar, suka taimaka wajen sauya da dama. Rashin kudin shigar cikin gidan da ma rushewar darajar Naira dai, na shafar kokarin sauke nauyin kula da bangaren lafiya da ma ilimi a mafi yawan jihohin kasar. Abun kuma da ke zaman kadangaren bakin tulu, a tsakanin miliyoyi cikin kasar da cimma moriyar tsarin dimukuradiyyar da kasar ke tafiya a kai.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani