Matsalar man fetur a Jamhuriyar Nijar
September 29, 2026
Jihohin Agadez, Damagaram da kuma Maradi su ne suka fi fuskantar wannan matsala ta karancin man fetir a jamhuriyar ta Nijar a baya bayan, inda masu ababen hawa kan share tsawon sa'o'i suna bin layin kafin kai wa ga samun man, biyo bayan matakin da wasu gwamnonin suka dauka na haramta sayar da man akan titina, da kuma kayyade adadin man da ake siyarwa jama'ar.
Halin da ake ciki a jihohin kasar
A Damagaram ma da akasari masu ababen hawan kan yi dogaro da man kan layin duk kanwar ja ce, sai dai babbar matsalar da masu sana'ar adaidaita suka fi kokawa har ta kai su ga yin jerin gwano zuwa gidan sarkin Damagaram dan kai mishi kukan su, yadda suka ce ana nuna musu bara-bara a gidajen man kafin saida musu shi. Amadou Moussa Ousmaniya shi ne shugaban kungiyar masu 'adaidaitan' a Damagaram wanda yake cewa mafi yawanci ana daukar 'yan adaidaita sahu kamar ba 'yan jiha ba, ana cin zarafinmu.
A jihar Agadez ma da ke arewancin kasar matsalar ta munana, kuma matashi Abdoul Aziz Abdoulahi shugaban kungiyar masu adaidaita a jihar ya ce su ne suka fi dandana kudar su dan haka ya yi kira ga mahukuntan kasar da su dauki matakin da ya dace.
Matsalar ta kasaita
Tuni dai wannan matsala ta fara shafar al'amuran yau da kullum na al'umma, inda wasu kan hakura da wasu damarmakin aiki da suke samu sakamakon tsadar sufuri da ake fuskanta a halin yanzun. Mahamdou Moussa da aka fi sani Bambino, daya ne daga cikin wanda wannan matsala ta kawo wa cikas a cikin ayyukansu inda ya ce sun shiga mawuyacin hali.
Wannan matsala dai ta biyo bayan karin matakkan tsaurara tsaro da sanya ido ne kan gidajen man da gwamnatin mulkin sojan kasar ta dauka da kuma tashin farashin man a makwabciyar kasar Najeriya, wanda a baya yawancin jihohin Nijar da ke da iyaka da ita sun fi dogaro da man nata ne akan na gida sakamakon saukin farashin sa.
A yanzu dai Jamhuriyar Nijar din kamar yadda wani rahoton bincike ya nunar a baya bayan nan, ita ce kasar da tafi ko wace a yammacin Afirka saukin farashin man, sai dai rashin wadatuwar sa a gidajen man kasar na kawo wa wannan matsayi tarnaki.