1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karancin man fetur na janyo cikas a Najeriya

February 9, 2018

A kokarin maganta matsalar man fetur a Najeriya, hukumar kula da rabo da sayar da albarkatun man fetur ta rufe wasu gidajen mai tare da tilasta wasu sayar da makamashin bisa farashin da gwamnati ta kayyade.

Nigeria Tankstelle in Lagos
Wani dan bumburutu dauke man feturHoto: AFP/Getty Images/E. Arewa

Yayin da matsalar karancin man fetur da ake fama da shi ya haifar tsaiko a harkokin yau da kullum a shiyar arewa maso gabashin Najeriya, hukumar kula da rabo da sayar da albarkatun man fetur  wato DPR ta rufe wasu gudajen mai tare da tilasta wasu sayar da man bisa farashin da gwamnati ta kayyade. Duk da gidajen masu yawa da ake da su a jihohin arewa maso gabashin Najeria da kuma kokarin da hukumomi ke yi na wadatar da gidajen man da albarkatun man, ana ci gaba da samun karancinsa da abin da ya sa farashin harkokin sufuri da abubuwa su ka yi tashin gwauron zabi. Yanzu haka dai a Maiduguri matsalar ta fi ta'azzara inda mutane suka zabi tafiya a kafa maimakon hawa motocin haya ko kuma babura masu kafa uku da ake kira Keke NAPEP, inda wasu kuma ke kasa sayen kayan abinci saboda suka yi tsada.

Kasuwar bayan fage na ciHoto: picture-alliance/ dpa


Bisa wannan ne ya sa hukumar kula da rabo da sayar da albarkatun man fetur  wato DPR ta dauki mataki kan gidajen man domin sa ido kan yadda suke sayar da man da kuma bankado masu boye shi ko karkatar da shi zuwa kasuwar bayan fage. Kunnen kashi da wasu gidajen sayar da man suka yi ya sa hukumar yayin zagawa a Maiduguri, ta rufe wasu gidajen mai uku tare da tilasta wasu sayar da man bisa farashin da gwamnati ta kayyade wasu kuma ma tauye maunin sayar da man su ke yi yayin sayar da man. Alhaji Idris Ali Zoaka, shi ne babban darakta mai kula shiyar arewa maso gabashin Najeriya na hukumar kula da rabo da sayar da albarkatun man fetur wato DPR ya ce tilas sai an tsaurara matakai.

Hoto: AFP/Getty Images/P. U. Ekpei

Kafin daukar matakin, masu gidajen mai na sayar da litar mai sama da Naira 250 sabanin farashin da gwamnati ta kayyade wato Naira 145. Matakin dai ya yi tasiri na wani lokaci don kuwa gidajen mai da dama sun dauki tsawon lokaci na sayar da man bisa farashin gwamnati. Hukumar ta DPR dai ta fadada wannan aiki zuwa sassan jihohin arewa maso gabashin Najeriya da nufin tabbatar da ana sayarwa jama'a man bisa farashin gwamnati da kuma magance karkata makamashin zuwa kasuwanni bayan fage.