1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kotun ECOWAS ta saka ranar hukunci kan Jamhuriyar Nijar

Uwais Abubakar Idris SB/LMJ
November 21, 2023

Kotun kasashen Afrika ta Yamma ECOWAS ta saurari shari'ar da Jamhuriyar Nijar ta shigar tana kalubalantar halacin takunkumin tattalin arzikin da kasashen kungiyar suka kakabawa kasar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi:

Zanga-zangar goyon bayan sojojin da suka kwace madafun ikon Jamhuriyar Nijar
Zanga-zangar goyon bayan sojojin da suka kwace madafun ikon Jamhuriyar NijarHoto: DW

Gwamnatin jamhuriyar Nijar mne da wasu mutane bakwai suka tunkari kotun a kan wannan al'amari da suka bayyana ya karya kaida da ma dokokin kungiyar ta Ecowas, domin sun shaidawa kotun cewa alammura  fa sun munana ainun ga 'yan kasar wadanda a zahiri ba su da laifi, domin ba su ne suka yi juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin jamhuriyar Nijar ba. Sun shaidawa kotun cewa takunkumin ya yi dalilin mutuwar mutane 142 ciki har da mata da yara kanana saboda rashin magunguna.

Karin Bayani: Nijar: Kotun shari'ar 'yan kasa da gwamnati

Sojojin da suka kwace madafun ikon Jamhuriyar NijarHoto: Balima Boureima/AA/picture alliance

Tun a ranar 31 ga watan Augusta ne ECOWAS ta sanya wa Jamhuriyar Nijar takunkumi bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 26 ga watan Yulin bana. A nashi bamgaren lauyan da ke kare kungiyar ta ECOWAS Maître Kanga Francois wanda ta yanar gizo ya kare kungiyar a shari'ar ya bayyana cewa kifar da gwamnatin dimukuradiyya laifi ne da ya sabawa kudurin kungiyar da na kasa da kasa wanda gwamnatin Jamhuriyar Nijar din ta sanya hannu tare da amincewa da shi, don haka karar da kasar ta shigar a kan batun takunkumi baya da wani hurumi.

To sai dai ga Maître Ismaril Tambo Musa daya daga cikin lauyoyin da ke tuhumar lamarin ya ce akwai bukatar fahimtara lamarin da ya shafi take hakkin jama'a na mutanen Jamuriyar Nijar.

Alkalin da ya jagoranci zaman kotun mai shari'a Edward Amoako Asante ya ce muhimmanci da kotun ta bai wa shari'ar ya sanya hanzarta saurarenta. Don haka alkalin ya tsayar da ranar 7 ga watan Disamba domin yanke hukunci a kan bukatar kotu ta tilastawa ECOWAS ta janye takunkumi har sai an warware matsalar.