1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Karar harbin bindigogi a filin jirgin Diori Hamani na Nijar

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 18, 2026

Ko a cikin watan Janairun 2026 'yan kungiyar ta'addanci ta IS sun kai hari filin jirgin saman na Diori Hamani na Yamai.

Filin jirgin sama na Diori Hamani a Jamhuriyar Nijar
Filin jirgin sama na Diori Hamani a Jamhuriyar NijarHoto: Zheng Yangzi/Xinhua/IMAGO

An wayi gari gari da jin karar harbe-harben bindiga a filin jirgin saman Diori Hamani na Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar a wannan Alhamis, watanni biyar bayan fuskantar makamancin farmakin masu ikirarin jihadi.

Wani mazaunin kusa da filin jirgin saman ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa AFP ta wayar tarho cewa ya fara jin amon bindigogin ne da karfe shida na safe, daidai da karfe biyar na asuba agogon GMT.

Karin bayani:An ji tashin bama-bamai a birnin Yamai na Nijar 

Ko a cikin watan Janairun 2026 'yan kungiyar IS sun kai hari filin jirgin saman na Diori Hamani, inda dakarun sojin Nijar da hadin gwiwar takwarorinsu na Rasha suka mayar da martani domin dakile farmakin, inda suka halaka 'yan ta'adda 20, ko da yake sojoji hudu sun samu raunuka.