1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Takun saka kan kundin tsarin mulki

Suleiman Babayo AH
April 25, 2024

'Yan adawa da kungiyoyin fararen hula sun shigar da kasar Togo a gaban kotun ECOWAS domin dakile fara amfani da kwaskwarimar da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar da ke yankin yammacin Afirka.

Shugaba Faure Gnassingbe na kasar Togo
Shugaba Faure Gnassingbe na kasar TogoHoto: Filip Singer/EPA Pool/dpa/picture alliance

Jam'iyyu adawa na kasar Togo da ke yankin yamamcin Afirka sun shigar koke a kotu game da yunkurin shigar da gyara ga kundin tsarin mulki da zai bai wa Shugaba Faure Gnassingbe damar fadada wa'adin mulkinsa.

Kungiyoyin fararen hula da jam'iyyun siyasa 13 suka shigar da karar a gaban kutun kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS, inda suke zargin gwamnatin ta Togo da karya ka'idodjin tsarin dimukaradiyya na kasar.

Gyare-gyaren kundin tsarin mulkin da majalisar dokokin wannan karamar kasa ta amince, sun kunshi mayar da kasar daga tsarin zaben shugaban kasa kai tsaye zuwa yadda majalisar dokoki za ta zabi shugaban kasa. 'Yan adawa suna zargin majalisar dokokin ba ta da hurumi, saboda wa'adin majalisar ya kare yayin da aka jinkirta zabe.

Tun shekara ta 2005 Faure Gnassingbe yake kan madafun ikon kasar ta Togo inda ya gaji mahaifinsa wanda shi ma ya shafe kimanin shekaru 40 yana mulkin kasar.