Yarjejeniyar kare 'yan gudun hijira
December 17, 2018Talla
Babban zauren mashawartar Majalisar Dinkin Duniya ya amince da yarjejeniya kan 'yan gudun hijira tsakanin kasashen duniya, mako guda bayan amincewa da irin wannan yarjejeniyar. Kusan kasashe 170 suka yi alkawarin taimakon mutanen da suke tserewa daga yaki da hukuba.
Fiye da mutane milyan 24 suke gudun hijira kimanin rabi suna kasa da shekaru 18 da haihuwa a cewar alkaluman Majalisar Dinkin Duniya. Kasashen duniya 10 suka karbi bakuncin kashi biyu bisa uku na daukacin 'yan gudun hijira.