1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kare yara 'yan makaranta a Najeriya

Uwais Abubakar Idris SB/AMA
June 22, 2023

A Najeriya kungiyar kare hakin jama'a ta Amanesty International ta bayyana bukatar daukan matakan gaggawa domin shawo kan matsalar galazawa yara dalibai da ke makarantu azaba.

Afirka Najeriya 'yan makaranta
'Yan makaranta a NajeriyaHoto: Yusuf Ibrahim Jargaba/DW

An dai tsara makarantun boko na kwana da ma wadanda ake zuwa daga gida don su zama wurare da dalibai za su samu salama da aminci, musamman a mu'amalarsu da malamai da ke zama iyaye a gare su. To sai dai akasin haka ne ke faruwa a wasu marakatun firamare da na sakandare, inda ake samun matsaloli na galazawa yara azaba da cin zarafinsu da kan kai ga mutuwa a wasu lokuta. Wannan ne ya dauki hankalin kungiyar kare hankin jama'a ta Amnesty International da ta tattauna matsalar da niyyar daukan matakan gyara. Mallam Isa Sanusi shi ne darakta kungiyar a Najeriya wanda ya ce ana samun karuwan matsalar take hakkin dan Adam a makarantu.

Karin Bayani: Najeriya: Jihar Borno ta saka hannu kan dokar kare yara

Makaranta a NajeriyaHoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Akwai dai iyayen yaran da irin wannan matsala ta shafa da idanunsu cike da hawaye a kan halin da suka shiga, domin zargin cewa hukumomin makarantun na kare wadanda suka aikata laifin tare da hadin bakin ‘yan sanda. Vivienne Akpagher ita ce mahaifiyar Karen Akpagher da aka yi wa fyade a makarantar firamere ta Premier da ke Abuja, fyaden da ya yi dalilin mutuwarta, wadda kuma ta nuna irin takaicin abin da ya faru da rudanin da ta shiga.

Amma me ke haifar da wannan matsala da matakan da ya kamata a dauka sanin cewa nauyi ne na hukuma ta kare dalibai a makarantunsu?  Muhammad Kusharki shi ne shugaban sashin kula da jinsi na hukumar kula da ilimin sakandare ta Abuja wanda sai an tashi tsaye. Akwai kungiyoyin da ke kare afkuwar wannan matsala a Najeriyar da suka bayyana girman matsalar da ma illarta.

Abin da ke daga hankali shi ne mumunar illar da wannan matsala za ta haifar ga Najeriyar da ke kokuwar rage yawan yaran da ba sa zuwa makarantar boko, domin hukumar ilimi da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa yawansu ya kai milyan 20.