Karfafa amfani da kayan gida a Jamhuriyar Nijar
March 26, 2026
Tun dai a wani taro ne da ya hada ministan kula da harkokin kasuwanci na kasa da yan kasuwa manya da kanana na kasar ta Nijar, aka tattauna batutuwan da suka shafi dafa wa 'yan kasuwa na cikin gida ta yadda za su samar da kamfanoni kuma su dauki mutane da dama aiki a cikin gida, kuma wannan batu na haramta wa ma'aikatun gwamnati sayo kayayyaki daga waje idan har ana yi a cikin gida na daga cikin wannan tsari.
Bangaren 'yan kasuwa
Da yake magana dangane da wannan mataki da gwamnati ta dauka, Alhaji Yacouba dan Maradi, daya daga cikin jagororin kungiyoyin 'yan kasuwa na kasa, ya ce yanzu ta rage ga 'yan kasuwa manya da kanana su dubi yadda za su hada kai domin cin ribar wannan mataki dan ci-gaban harkokin kasuwanci da masana'ntu a kasar ta Jamhuriyar Nijar.
Matakin dai na gwamnati ya kuma kira ga 'yan kasuwa da sauran masu zuba jari da su yi hubbasa wajen ganin sun bunkasa harkokinsu na kamfanoni ta hanyar sarrafe-sarrafe. Ismael Adamou Harou matashi da ke ayyukan noma kaman na shinkafa, rake da ma rogo, ya dubi wannan mataki na gwamnati kuma ya yaba sosai duk da cewa akwai kalubale.
Masu sharhi sun yaba
A fuskar masu sharhi irin su Habila rabiou matrashin dan siyasa da ke da burin ganin an samu babban sauyi na ci gaba ya ce lalle an yi sakaci mai yawa a baya.
Abin jira a gani dai shi ne matakin da su kansu 'yan kasuwa musamman masu hannu da shuni za su dauka wajen ganin sun girka manyan masana'antu da ka iya tallafa wa kananan masana'antu da matasa ke kirkira a kasar ta Jamhuriyar Nijar.