1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU da Afirka za su karfafa huldar kasuwanci

Abdullahi Tanko Bala
November 24, 2025

Nahiyar Turai da Afirka na bukatar juna fiye da kowane lokaci a baya yayin da duniya ke fuskantar kalubale - Inji Von der Leyen

 Südafrika, Kapstadt - 8. EU-Südafrika Gipfel
Hoto: Esa Alexander/REUTERS

Shugabar hukumar tarayyar Turai Ursula Von der Leyen ta baiyana haka a taron kolin kungiyar tarayyar Turai da Afirka da ke gudana a Luanda babban birnin kasar Angola.

Von der Leyen ta ce dole ne nahiyoyin biyu su karfafa kawancen tattalin arziki a wannan zamani da shingen cinikayya ke tarnaki ga shigar da kaya a tsakanin kasashe.

Shugabar hukumar tarayyar Turan ta kara da cewa tana ganin damammaki masu yawa na fadada harkokin kasuwanci duk da cewa kashi daya cikin kashi uku na kasashen Afirka suna fidda kayayyakin su zuwa nahiyar Turai.

A taron kolin Turai da Afirka da ya gudana shekaru uku da suka wuce an cimma kudirin Tarayyar Turai za ta fadada zuba jari a Afirka da ya kai na euro biliyan 150 kwatankwaci dala biliyan 173 nan da shekarar 2027 a cewar Von der Leyen.