Lafiya
Matakan yaki da cutar Coronavirus a Asiya
January 21, 2020Talla
Tun bayan da hukumomin Beijing suka sanar da cewa bincike ya tabbatar da ana kamuwa da cutar ta Coronovirus daga mutum zuwa mutum, hukumomi daga Hong-Kong zuwa Singapor da Ostareliya, sun karfafa matakan bincike a filayen jiragen sama.
A wannan Talata kadai hukumomin kasar ta Chaina sun sanar da gano karin wasu mutane 77 da suka kamu da cutar wanda ya kai adadin mutanen da suka kamu da ita zuwa 300 a kasar a yayin da ake sa ido kan wasu marasa lafiya 922 da ake zargin sun harbu da cutar ne.
An kuma samu karin wasu mutane uku da cutar ta halaka a birnin Wuhan na tsakiyar kasar da ke zama tushen bayyanar wannan cuta wacce ta harbi mutane da dama a kasashen Japan da Koriya ta Kudu da kuma Thailand.