Burkina da Mali za su karfafa matakan tsaron iyakokinsu
August 27, 2019Talla
A yayin da yake ganawa da firaministan Burkina Faso Christophe Dabiré a yammacin jiya, ministan tsaron Mali Janar Ibrahima Dembélé, ya ce tuni bangarorin kasashen biyu suka fara kaddamar da tsaron iyakokinsu na hadin gwiwa, a wani yunkuri na kawo karshen hare-haren ta'addancin da ke addabar kasashen biyu da kuma suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.