1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karfafa yaki da ta'addanci tsakanin Najeriya da Amirka

April 30, 2018

Shugaban Muhammadu Buhari na Najeriya ya gana da takwaransa na Amirka Donald Trump inda suka bayyana shirin karfafa kasuwanci da magance matsalolin tsaro da ake samu a Najeriya.

Kombobild Donald Trump und Muhammadu Buhari
Shugaban Amirka Donald Trump da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari

Masu zanga-zangar nuna adawa da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriyar da ma masu nuna goyon baya gareshi dai, sun yi riga malam masallaci a wajen tattaunawar, domin kuwa sun gudanar da zanga-zangar ne gabanin ganawar Trump din da Buhari. Duk da cewar dai  tsohon shugaban kasar Amirkan Barracks Obama ne ya taimaka wajen tabbatar da sauyin da al'ummar Tarayyar Najeriya suka zaba shekaru Uku baya, daga dukkan alamu Shugaba Trump da ke kai yanzu ne ke shirin agazawa Buharin wajen tabbatar da cika alkawuran da ke tsakaninsa da 'yan zabe na kasar. Ana dai sa ran  wata ganawa ta shugabannin biyu a birnin Washington za ta yi tasiri ga muhimman bukatun Tarayyar Najeriya na samar da tsaro da kuma nasarar kwato dukiyar haramun ta 'yan kasar daga ke boye a kasashen duniya daban-daban.

Tsaro da tattalin arziki ne kan gaba a tattaunawar

Wata sanarwar da Abujar ta fitar dai ta ce ziyarar da za a kamalla ta bisa teburin abincin rana, za ta mai da hankali ga kulla kawance na tsaro da yaki da ta'addanci sannan kuma da kokari na ingantar tattali na arzikin Tarayyar Najeriyar. Ana kuma sa ran zuba jarin kamfanonin na Amurka a cikin harkar noma da samar da abincin Tarayyar Najeriya, kasar da a yanzu ke kokarin raba kafa daga harkar man fetur din da ke neman kai ta cikin rikici. Ko bayan nan dai Tarayyar Najeriyar na shirin wata yarjejniyar zuba jarin dalarAmirka miliyan dubu biyu, da nufin sake farfado da layin dogon da ya hade Kano da Ikko sannan da Maiduguri da Fatakwal.