Karfin soji ba zai magance rikicin Iran ba-Tehran
October 5, 2026
Da yake jawabi a wani taron jakadun kasashen waje, Araghchi ya ce idan abokan gaban Iran suka sake zabar hanyar fafatawa ta soji, Tehran za ta mayar da martani da karfi fiye da na da.
Ya jaddada cewa ko yakin ko kuma sabbin takunkumai ba za su iya magance rikicin ba, inda ya bayyana cewa hanya mafita daya ita ce ta diplomasiyya bisa adalci.
A gefe guda kuma hukumar tsaron ruwa ta Birtaniya UKMTO ta bayar da rahoton cewa wani jirgin dakon mai a mashigin ruwa na Hormuz ya gamu da bugun wani abu da ba a san ko menene ba, lamarin da ya haifar da lalacewar wani bangare na injin jirgin.
UKMTO ta bayyana cewa ma'aikatan jirgin suna cikin koshin lafiya kuma ba a samu rahoton wata illa ga muhalli ba.
Ba ta bayar da cikakkun bayanai game da ranar da lamarin ya faru ba, ko kuma inda jirgin ya taso ko inda ya nufa.
Karin Bayani: Iran ta sanya sharudda bakwai na bude mashigin Hormuz