Karim Wade ya shiga hannun hukumomi
April 18, 2013An jefa Ɗan tsohon shugaban ƙasar Senegal Abdoulaye Wade a gidan kaso bayan da kotu ta tuhume sa da lafin cin hanci da rashawa, inda ake zargin ya kwashi dukiyar da ya kai yawan miliyan dubu guda na euro.
Karim Wade wanda ya riƙe muƙaman gwamnati daban-daban lokacin da mahaifinsa ke mulki, ya tafi gidan kason ne cikin tsauraran matakan tsaro, kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana.
Wasu mutane bakwai da ake zargi da hannu wajen yin sama da faɗi da dukiyar ƙasar kuma na tsare a hannun hukumomin.
Ana zargin Karim Wade mai shekaru 44 na haihuwa, da mallakan manyan kamfanoni da gidaje a gida da waje ta hanyoyin da basu dace ba, waɗanda suka haɗa da kamfanin da ke kula da shige da ficcen kayyaki a babbar tashar Containan da ke babban birnin ƙasar wato Dakar da ma wani bankin Morocco mai suna BCME
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu