1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Karin kafafen yada labarai

Muhammad Bello LMJ
September 29, 2021

Gwamnatin Najeriya ta bayar da lasisin kafa sabbin tashoshin radio da talabijin kimanin 159 masu zaman kansu. Adadin tashoshin radiyo da talabijin a Najeriya ya kai 625, bayan bayar da lasisi ga wasu sababbin tashoshi.

Schild on Air Studio Mischpult
Ana samun karuwar gidajen radiyo da talabijin ma sua zaman kanusu a NajeriyaHoto: On-Air/Fotolia

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne dai ya sanya hannu, domin yarjewa wadanda ke da bukatar kafa sababbin tashoshin radiyo da talabijin din masu zaman kansu a kasar kimanin har 159. Wadanda gwamnatin ta sahalewa bude tashoshin talabijin da radiyon dai, sun hadar da kamfanoni masu zaman kansu da manyan makarantu kamar jami'o'i da kwalejojin kimiyya da fasaha da kuma wasu yankunan da kan bude gidajen radiyo na  al'umma wato Community Radio.

Kafafen sada zumunta na zamani, na taka rawa a fagwen yada labaraiHoto: Sefa Karacan/AA/picture alliance

Za a iya cewar kafafen yada labarai na talabijin da radiyo na da kalubale babba, wajen ganin sun bi ci-gaban fasahar zamani ta kafar Internet wato kafafen sada zumnta na zamani, inda akasari ake samun labaran bogi da ke cin karensu babu babbaka. Mafi  yawan al'umma dai na dogara da kafafen, wajen ji ko ganin labarai. Wannan ya sa da daman kafafen yada labarai na talabijin da radiyo a Najeriyar, samarwa kansu dandalin yada shirye-shiryensu. Babban dai aiki ga Hukumar Kula da Kafafen Yada Labarai ta Kasa a Najeriyar wato NBC, shi ne tabbatar da cewar wadannan kafafen yada labaran na bin dokokin kasa da ka'idojin kafa su kuma abin da mutane da dama ke fatan ganin NBC din ta dage a kai ke nan.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani