Karin takunkumi kan Rasha
July 30, 2014Talla
Amirka da Tarayyar Turai sun sanar da sabbin takunkumi kan gwamnatin Rasha bisa abin da ya shafi yakin gabashin Ukraine. Shugaban kasar Amirka Barack Obama shi ne ya sanar da karin takunkumin, inda a yanzu ya hada da makamashi da makamai da kuma fannin tattalin arzikin kasar ta Rasha.
Bisa wannan takunkumin daga yanzu kungiyar EU za ta daina sayar da wasu kayayyakin fasaha ga kasar Rasha, kana za su daina yin hulda da wasu bankuna wadanda ke mallakar gwamnatin kasar.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Suleiman Babayo