Karol Nawrocki ya lashe zaben shugaban kasar Poland
June 2, 2025
Talla
Hukumar zaben Poland ta ce, dan takarar jam'iyyar adawa mai ra'ayin 'yan mazan jiya, Karol Nawrocki ya lashe zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da kashi 50.89 na kuru'un da aka kada.
Abokin hammayarsa, Rafal Trzaskowski na jam'iyyar masu sassaucin ra'ayi kana magajin garin Warsaw na da kashi 49.11 cikin 100. Yayin yakin neman zabensa, Nawrocki mai shekaru 42, wanda masanin tarihi ne ya yi alkawarin fifita tabbatar da manufofin tattalin arziki da zamantakewa a kan 'yan Poland fiye da sauran 'yan kasashen waje.
Sai dai ana ganin hakan zai kawo tarnaki ga wasu 'yan siyasar kasar masu sassaucin ra'ayi sakamakon yadda shugaban kasa ke da ikon amince da kudurin doka.