1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karol Nawrocki ya zama shugaban kasar Poland

Mouhamadou Awal Balarabe
June 2, 2025

Dan takara mai ra'ayin rikau ya samu nasara da a zaben shugaban kasar Poland da kashi 50.89% na kuri'un da aka kada yayin da abokin hamayyarsa Rafal Trzaskowski mai saussaucin ra'ayi ya tashi da 49.11%.

Karol Nawrocki
Hoto: Jakub Porzycki/Anadolu/picture alliance

Sabon shugaban na iya kawo cikas ga yunkurin gwamnati mai ci na taimaka wa Ukraine da kuma neman mutunta manufofin Kungiyar Gamayyar Turai. Dan takara na gwamnnatin Poland Rafal Trzaskowski da kansa ne ya yi wa abokin hamayyarsa Karol Nawrocki barka da arziki, bayan da aka kalailacen duk kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasa.

Wannan ya nuna cewar kusancin da magajin garin Warsaw yake son samarwa da EU dasauye-sauyen tsarin iyaliza su bi ruwa. A daya bangaren kuwa, nasarar Karol Nawrocki, a cewar manazarta, za ta karfafa jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya ta PiS, wacce ta yi mulki Poland tsakanin 2015 zuwa 2023. Saboda haka ne ake ganin cewar Nawrocki zai iya kawo cikas ga alaka ta kut da kut da take da ita da makwabciyarta Ukraine, saboda Nawrocki na sukar manufofin kungiyar tarayyar Turai EU da kungiyar tsaro ta NATO, kuma yana son rage karbar 'yan gudun hijirar Ukraine. Dama zababben shugaban, wanda ke goyon bayan manufofin Donald Trump, ya yi ikirarin samun goyon bayan shugaban na Amurka.

Duk da cewa firaminista ne ke rike da akalar gwamnatin Poland, amma shugaban kasa na da tasiri kan manufofin ketare da kuma tsaro. Hasali ma dai, yana iya hawa kan kujerar naki a matakin majalisa musamman abin da ya shafi doka. Wannan ne ma ya sa shugaban mai barin gado Andrzej Duda ya murkushe sauye-sauye da dama da Firayiminista Donald Tusk ya sa a gaba ciki har da neman halarta auren jinsi da zubar da ciki.

Hoto: Petr David Josek/AP/dpa/picture alliance

Alal hakika ma dai, ana ganin cewar Karol Nawrocki zai dora ne inda shugaba mai barin gado ya tsaya. Dama magoyansa na neman ya tsaurara dokokin shige da fice da kuma nesanta kasarsu daga manufofin na Kungiyar Tarayyar Turai. Shugaban kasar Poland mai barin gado Andrzej Duda ya shaida wa manema labarai cewa tsaro ya taka muhimmiyar rawa a zaben da aka gudanar a jiya Lahadi.

Ya ce "Gina dangantaka ta kut da kut tsakaninPoland da Amurka da kuma tabbatar da tsaronmu a kan wannan ginshiki, da kuma karfafa tsaronmu ta hanyar karfafa sojojin Poland ta hanyar kashe kudade a harkar tsaro, ta hanyar karfafa karfin kasarmu ta hanyar daidaitaccen ci gaban Poland: Wannan ita ce alkiblar da 'yan Poland suka zaba a kuri'un da suka kada a jiya. Muna gode muku sosai. Ina alfahari da haka."

Shugabannin kasashen waje da dama sun taya Karol Nawrocki murnar nasarar da ya samu. Shugabar hukumar zartarawa ta Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta bayyana kwarin gwiwa da fatan samun hadin kan fadar mulki ta Warsaw wajen ci gaba da gudanar da aiki tare.

A nasa bangaren, shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya yi kira ga kasashen Poland da Jamus da su ba da hadin kai bisa tsarin demukuradiyya da doka da oda domin tabbatar da makomar Turai ta fuskar tsaro da 'yanci da wadata. Shi kuwa firaministan Hungary Viktor Orban, wanda ke da tsaurin ra'ayin siyasa, ya bayyana nasarar da Karol Nawrocki ya samu a matsayin "abin ban mamaki."

Hoto: Aleksandra Szmigiel/REUTERS

Shugaban Poland mai barin gado Andrzej Duda ya ce dole negwamnatin Donald Tusk ta yi la'akari da muhimman alkawuran da Karol Nawrocki ya yi a lokacin yakin neman zabensa, saboda ya samu goyon bayan 'yan Poland

Ya ce "Wadannan matakai na wuyar shugaban kasa, ko shakka babu, da kuma wuyar gwamnati. Ko gwamnati za ta so yin aikin hadin gwiwa, ko za ta so yin aiki da kyau da shugaban kasa? Ina fatan hakan ya kasance ga Firayiminista Tusk da gwamnatinsa. Wannan bayyanannen sako ne da 'yan Poland suka mika, da ke tsammanin irin wannan manufar akasarinsu, kamar yadda zababben shugaban kasar ya gabatar, kamar yadda aka aiwatar a lokacin yakin neman zabe na Karol Nawrocki."

Poland, kasa ce mai mutane miliyan 38, tana samun bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri, kuma tana taka muhimmiyar rawa a harkokin diflomasiyyar kasa da kasa musmmana a yakin Ukraine. Galibin makamai da agajin kasashen yammacin duniya da ake aikawa Kyiv na bi ta kasar Poland.