1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iritiriya da Habasha za su sasanta

Gazali Abdou Tasawa Abdul-raheem Hassan
June 20, 2018

Shugaban kasar Iritiriya Issaias Afeworki ya sanar da shirin tura jami'an kasarsa zuwa Habasha domin gabatar da tayin sulhu dan wanzar da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu.

Demonstration gegen die eritreische Regierung in Addis Abeba
Hoto: DW/Yohannes G/Egziabher
Firaiministan Habasha, Abiy AhmedHoto: DW/Y.Geberegziabher

A jawabin da ya gabatar albarkacin ranar tunawa da 'yan kasar Iritiriya da suka rasa rayukansu a lokocin yakin neman 'yancin kasar daga Habasha, shugaban kasar ya sanar da aniyar a matsayin amsa ga kyakkyawar aniyar da sabon firaministan kasar Abiy Ahmed ya nuna ta neman zaman lafiya da kasar. Shugaba Assaias ya bayyana dalillansa na yi wa abokiyar gabar tasu wannan tayi na zaman lafiya:"Kamar yadda ta ke a nan Iritiriya, al'ummar Habasha na begen zaman lafiya da kaunar juna da makobciyarsu. Kuma kyawawan kalamai da ke fitowa daga bakin magabatan kasar a baya-bayannan shaida ce ta bukatar zaman lafiya daga al'ummar kasar. Dan haka ne za mu aika da wata tawaga a birnin Adis Ababa domin auna girman ci gaban da aka fara samu kan batun zaman lafiya tsakanin kasashen biyu ta yadda za mu kai ga samar da wani tsari na ci gaba da karfafa wanann turba da muka hau."

Shugaban kasar Iritiriya, Isaias AfwerkiHoto: Eritrea Minister of Information/Y.G. Meskel

Tuni dai fadar shugaban kasar Habasha ta yi marhabin da tayin zaman lafiya daga kasar Iritiriya, inda a wani sako na babban daraktan fadar shugaban Habashar ya wallafa jim kadan bayan sanarwar shugaban Iritiriyan ya ce a shirye suke su yi wa tawagar kyakkyawan tarba. Dama dai tun a farkon wannan watan Yuni, sabon Firaiminitan Habashan Abiy Ahmed ya bayyana aniyar soma aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da kasashen biyu suka cimma a shekarar 2000 a birnin Algeriers tare da mika wa kasar ta Iritiriya birnin Badme kamar yadda kwamitin raba gardama na kasa da kasa kan rikicin iyaka ya tsayar. Kuma shugaba Issaias na Iritiriya ya ce lokaci ya yi da kasashen biyu za su dakatar da rikici a tsakaninsu, musamman ta la'akari da yadda aka kai matsayin da biri ya gaji mai gona ya gaji: "Shekaru 27 ba kwanaki 27 ba ne. Asarar rayuka da dukiyoyin da kasashenmu suka yi a cikin wannan yaki ta isa. Kuma a zahiri ta ke Habasha ta ji jiki sosai, inda ta kai al'ummarta ta soma daga murya tana neman a kawo karshen wanann rikici. Wannan ya yi sanadiyyar faduwar jam'iyyar TPLF wacce ta jima tana rura wutar gaba tsakaninmu da Habasha. Amma yanzu duk wannan ya zamo tarihi Habasha ta bude sabon babin siyasa da na shugabanci."

Rikicin iyaka da ya barke tsakanin kasashen biyu, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla dubu 80 daga shekara ta 1998 zuwa 2000. A shekarar 2002, wani kwamitin shiga tsakani ya bayyana birnin Badme a matsayin yankin kasar Iritiriya, sai dai Habaha ta ki mika birnin wanda har yanzu take ci gaba da mallakewa tare da jibge tarin sojoji a cikinsa. Birnin da kuma a yanzu sabon Firaministan Habasha ya ce a shirye yake ya mika wa Iritiriya shi wanda kuma ke kasancewa tushen wannan turbar zaman lafiya da kasashen biyu 'yan uwan juna kuma abokan gabar juna suka kama.