Karshen gaba tsakanin Kiir da Marchar
January 22, 2015Talla
Gwamnatin Sudan ta Kudu ta kuma 'yan tawayen kasar sun cimma yarjejeniyar hadin kai, bayan da suka shafe watanni 13 suna kai ruwa rana tsakaninsu.Tattaunawar da ta gudana a Arusha da ke arewacin Tanzaniya, ta bayar da damar dinke barakar da ke tsakanin bangarorin SPLM dake gaba da juna.
Rikicin da ya barke tsakanin shugaba Salva Kiir da kuma tsohon mataimakinsa Riek Machar a kashen shekara ta 2013 ya haddasa mutuwar mutane sama da dubu biyu yayin da akalla mutane miliyan daya suka kaurace a matsugunansu.