1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafutika a shafukan intanet a Kenya

Julia Mielke/Aishat Bello Mahmud/YB May 25, 2016

Masu fafutuka a kafar sadarwa ta Intanet a kasar Kenya na son cin moriyar kafar ta fannin bunkasa tattalin arziki da zamantakewa sai dai a kwai barazana.

Juliana Rotich
'Yan fafutika ta intanet a birnin NairobiHoto: AFP/Getty Images

Amfani da fasahar ta intanet dai na kara samun karbuwa a kasar Kenya duk da irin kalubalen da ya yi wa fasahar dabai-bayi. Ga matashi Ole Shitemi wani mai fafutika a kafar sadarwar ta internet cewa ya yi shi kam fitar da bayanan da ya ke a kafar sadarwar ta Intanet ya fi karfin sha'awa, domin hanya ce ta samun abin masarufi kuma ya na sanar da al'umma halin da duniya ke ciki, shafukansa na da mutukar farin jini a wajen 'yan kasar.

"Babban kalubalen da nake fuskanta shi ne irin zargin da ake wa masu shafuka a kafafen intanet a Kenya na cewar ana biyan su kudade da zummar su bata sunan wasu."

A kasar ta Kenya dai akwai kimanin matasa dubu15, da ke yin wananan hada-hada ta intanet inda mafi yawa daga cikin na zaune a babban birni kasar na Nairobi. A shekaru biyar din da suka gabata ne dai masu wanannan fafutika suka kaddamar da kungiyarsu, inda suka rada mata suna BAKE.

Alamar sha'awa ta bin shafi a intanetHoto: Getty Images

James Wamathai darakta ne a kungiyar ta Bake ya bayyana cewa:

"Muna burin muga mutane daga wajen Nairobi na shigowa wannan kungiya, kamar yadda suke fadar labaransu a shafukan internet, bawai kawai don su bayyana wa duniya halin da yankunansu ke ci ba wai don ya zamo musu wata hanya ta samun kudin shiga."

Sai dai duk da kokarin da wadannan matasa ke yi don samawa kansu abin dogaro da kai, jami'an tsaron kasar ta Kenya na mamayar su inda suke kafa musu hujja da dokar kasar da aka sabunta kan 'yancin fadin albarkacin baki a shekaru biyun da suka gabata.