Fargabar karuwar kai hari a inda ake da dandazon jama'a
July 9, 2015Talla
Najeriya na ci-gaba da fuskantar karuwar hare-haren da ake dangantawa da 'yan kungiyar Boko Haram musamman a yankin arewacin kasar. Tun dagamakon da ya shige zuwa cikin wannan makon, rayuka masu yawa ne suka salwanta daga hare-haren da aka kai a garuruwan Yobe da Jos da Zaria, da ke yankin arewacin Najeriya, daura da wadanda suka jikkata.