1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar hare-hare a Siriya

May 19, 2012

Tsugune bata kare ba a Siriya sakamakon karuwar tashe-tashen hankula da yawaitar hare-hare. Lamarin da ya janyo zargin kungiyoyin ta'addanci da hannu wajen ta'azarar rikicin

Members from the United Nations observers mission in Syria survey the damage after an explosion in Deir Al-Zour, in this handout released by Syria's national news agency SANA, May 19, 2012. A suicide bomber carried out a car bombing in the eastern Syrian city of Deir al-Zor on Saturday, and killed nine people and wounded about a hundred people state television said. REUTERS/Sana/Handout (SYRIA - Tags: CIVIL UNREST POLITICS) THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS. FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS
Hoto: Reuters

Akalla mutane bakwai suka hallaka wasu 100 kuma suka yi rauni sakamakon fashewar bam a wata karamar mota ranar asabar a birnin Dair al zur, birni mafi girma a Siriya.

Gidan talabijin na kasa ya ce bam din ya fashe ne a kan wani titi da ke kusa da shelkwatar sojojin kasa da na sama da kuma asibitin soji.

Kamfanin dillancin labarun kasar na SANA ya ce karamar motar na makare da kimanin kilogram 600 na sinadarai masu fashewa, ya kuma kara da cewa tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ke sanya ido kan yadda ake aiwatar da kudurin tsagaita wutan da ta fara aiki ranar 12 ga watan Afrilun da ya gabata sun ziyarci wurin.

To sai dai dangane da irin wadannan hare-hare ga bayanin da mai magana da yawun babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Martin Nesirky ya yi karin bayani:

"A bayyane ya ke cewa hare-haren da aka kai a Damascus, wata kungiya ce wacce ke da manufofinta, kuma akwai damuwa kwarai, na cewa kungiyoyin ta'adda na amfani da cigaban tashe-tashen hankula a matsayin wata dama na gudanar da ayyukansu"

A halin da ake ciki kuma mashawarcin babban sakataren majalisar Dinkin Duniya kan batutuwan da suka shafi soji ya isa birnin Damascus inda zai fara ran gadi na kwanaki uku.

Masu sanya ido na cikin gida a kan rikicin, sun ce daga watan Maris na shekarar 2011 zuwa yanzu akalla mutane dubu 12 suka hallaka.

Mawallafiya: Pindo Abdu-Waba
Edita: Usman Shehu Usman