Karuwar hare-hare kan jami'an kiwon lafiya a Siriya
June 6, 2013Ganin irin wannan hali ne ya sanya kungiyar likitocin duniya tayi gargadin cewar matakan keta hakkin jama'a sun zama ruwan-dare a kasar ta Siriya, kuma kungiyar tayi kira ga gwamnatin Jamus tare da kawayenta na kungiyar hadin kan Turai su kara matsa lamba kan gwamnarin shugaban kasa Bashar al-Assad.
A yan makonnin baya ne wasu dauke da bindigogi suka harbe wani likita a garin Aleppo. Wani likita dan Siriya dake zaune a nan Jamus, wanda kuma baya so a ambata sunansa, saboda tsoron ramuwar gayya, yace yan sandan gwamnati a birnin na Aleppo sun shiga gidan da likitan yake duba marasa lafiya suka harbe shi, saboda yaki amincewa da hada kansa da rundunar sojan shugaba Bashar al-Assad. Tankred Stoeb, shugaban kungiyar likitocin duniya reshen Jamus yace a kasar ta Siriya ba wani sabon abu bane a kaiwa asibitoci da likitoci da marasa lafiya harin makamai. Jami'in yace kungiyarsa tana tafiyar da asibitoci biyar ne a Siriya.Yace ya zuwa yanzu ya zama wajibi a boye inda wadannan asibitoi suke, domin kare su da marasa lafiya dake zuwa neman magani cikinsu.
A yanzu haka dai, kusan kashi 60 cikin dari na asibitoci da kashi 80 cikin dari na motocin daukar marasa lafiya an lalata su, a tsawon shekaru biyu na yakin basasan kasar ta Siriya, yayin da tsarin kiwon lafiya gaba daya a wannan kasa yake kan hanyar rushewa. Stoeb, dake jawabi a wurin babban taron shekara na kungiyar likitocin duniya reshen Jamus a Berlin, yace halin tsaro a Syria ya shiga wani mummunan matsayi.
Yace babban abin da yafi kawo mana damuwa shine ganin cewar likitoci da marasa lafiya da asibitoci ana ci gaba da kai masu hare-hare, abin da ya sabawa dokokin kasa da kasa da kuma dokokin da suka tanadi kare marasa lafiya da masu fama da raunuka da likitoci da wuraren kula da marasa lafiya, tare da ganin cewar wadannan wurare, sabanin dokokin duniya, ba'a daukar su a matsayin wuraren da babu ruwansu da yaki, kuma suke bukatar kariya a Siriya.
Bisa l'ada dai dokokin duniya sun tanadi kariya ta musamman ga likitoci da asibitoci da marasa lafiya. Hakan yana nufin hatta a lokatai na tashe tashen hankula wajibi ne a karesu. To sai dai kungiyar ta likitocin duniya tace tun daga shekarun baya ta fara lura da wani yanayi dake zama abin damuwa: wannan bangare na dokar kasa da kasa da ta tanadi kariya ga masu bukatar kariyar ana kara yin watsi da ita. Tun a lokacin yakin Irak da na Libiya an rika kai hare-hare kai tsaye ga motocin daukar marasa lafiya da jami'an kiwon lafiya. Frank Dörner, jami'i a kungiyar ta likitocin duniya reshen Jamus ya nuna cewa:
A game da kaiwa asibitoci da ma'aikatan kiwon lafiya hare-hare, babu shakka mun lura da yadda hakan ya zama yar kullum. Mun lura da hakan tsawon shekaru da dama. A kasar Irak alal misali, an rika kaiwa motocin daukar marasa lafiya hari yayin da a kasar Libiya haka ma al'amarin ya kasance. Abin da yake dabam a kasar Siriya shine wadannan hare-hare sun zama ruwan dare kuma wadanda suke yinsu yanzu ma sukan fito fili ne su kai hare-haren.
Kungiyar ta likitocin duniya tace a yanzu tana bada taimakonta gaba daya ne a yankunan dake hannun yan tawaye, saboda gwamnati ta hana ma'aikatan kungiyar shiga yankunan dake hannun jami'an tsaronta. A game da yiwuwar amfani da makamai masu guba da Majalisar Dinkin Duniya take zargin gwamnatin Assad dashi, kakakin na kungiyar likitocin duniya yace ya zuwa yanzu, babu maras lafiya ko daya da aka kai asibitin dauke da wasu alamu na guba a jikinsa.
Mawallafi: Conrad/Umaru Aliyu
Edita: Mohammad Nasiru Awal