1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tripoli: Lugudan wuta kan fararen hula

Mahamud Yaya Azare
April 18, 2019

A kokarinsu na kame birnin karfi da yaji, dakarun Janar Khalifah Haftar na ci gaba da yi wa birnin Tripoli lugudan wuta, a daidai lokacin da kwamatin sulhun MDD ke nazarin halin da fararen hula ke ciki

Libyen Wadi Rabie Kämpfe bei Tripolis
Hoto: Getty Images/AFP/M. Turkia

 

Tun a daren Alhamis ne dai dakarun madugun 'yan tawayen Libiya Janar Haftar suka yi ta kai hari kan birnin Tripoli wanda ya kai ga halaka mutane 11 da jikkata gwammai a unguwannin Abu Saleem da Intisar, hare haren da mazauna birnin suka kira na 'yan ta,adda:

"Wannan azzalumin mutumin,J anar Haftar da yake harba rokoki kan fararen hular da basu ji ba basu gani ba, shi ne cikakken  dan ta,adda. Ya zama wajibi kasashen duniya su takamar birki. Abun takaici ma shine,wasu kasashen ketare makiya ne ke tallafawa wannan  dan tahaliki.

Tuni dai shugaban hukumar hadin kan kasa ta Libiyan, Fayeez Sarraj ya sha alwashin gurfanar da Janar Haftar gaban kotun duniya kan wannan aika aikar da ya ce yana tafkawa:

Mayakan Janar Janar Khalifa HaftarHoto: picture-alliance/AA/H. Turkia

"Hare haren dabbanci da rashin tausayin da Haftar ke jagorantar kaisu, manyan laifuffukan yaki ne da baza mu bari su wuce ba. Muna tara dalilai don gabatar dasu gaban kotun duniya, don a hukuntashi kan irin miyagun laifuffukansa na rashin imani.

To sai dai a nasa gefen, Janar Haftar a ta bakin kakakin rundunarsa, Ahmad Mismari ya musanta zarginsa da kai hare haren kan mai uwa da wabi kan fararen hula:

"Muna tabbatar da cewa, mayakan sa kai na yan ta,adda dake garkuwa da birnin Tripoli ne ke kai irin wadanan miyagun hare hare kan fararen hula. Muna kuma yin tir da irin wadannan ayyukan ta'addancin.”

  Wanannan somamen da Janar Haftar din da ke samun goyan bayan kasashen Masar da Emarat da Saudiya da Faransa da Rasha, ya faroshi makwanni biyun da suka gabata, ya jawo dakatar da tattaunawar sulhun da aka tsara za,a yita a tsakiyar wannan watan, kamar yadda ya raba kan yan kasar, da kawunan tsofin yan majalisarta.

A yayin da da shuwagabanin majalisar suka fito suka goyi bayan Janar Haftar kan wannan samamen, su kuwa galibin 'yan majalisar kira suke da a koma kan teburin shawara:

Janar Khalifa Haftar na LibiyaHoto: picture-alliance/dpa/M. Shipenkov

"Muna tofin Allah tsine ga wannan samamen cin zalin. Bama tare da jagororin majalisa kan halatta wannan cin zalin da sunan neman yanta Tripoli. Muna kira ga dakarun Haftar da su gaggauta komawa inda suke ada, don dakatar da zub da jini da komowa ga tautaunawar sulhuntawa".

Duk hakan dai na zuwa ne,adadai lokacin da kasar Jamus ta nemi kwamatin sulhu na MDD da ya zauna a yau, da nufin daukar matakan kar-ta-kwana don dakatar da zub  da jini a kasar ta Libiya.