Karuwar kin jinin 'yan Isra'ila da addini Islama
November 4, 2023Mr. Turk ya ce tun bayan harin ranar 7 ga watan jiya da kungiyar Hamas ta kai Isra'ila, ake ganin munanan kalaman tsana a shafukan sada zumunta da ma a tsakanin al'umma a bangarori daban-daban na duniya, abin tir ne da Allah wadai.
Kazalika shugaban na Hukumar kare hakkin Bil Adama ya ce Musulmai da 'yan Isra'ila na bayyana yadda rayukansu ke a cikin hadari, lamarin da ke tayar da hankali.
Ya kuma yi tsokaci a kan yadda kasashen duniya musamman na yammaci ke murkushe masu zanga-zangar adawa, inda ya ce hakan take hakki ne na al'umma.
An shiga mako na 5 ke nan tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da harin ramuwar gayya a kan Hamas biyo bayan harin da ta kai mata da ya hallaka Isra'ilawa 1,400, sama da Falasdinawa dubu 9500 ne ya zuwa yanzu ma'aikatar lafiyar Hamas ta tabbatar da mutuwarsu.
karin bayani: Ma'aikatar lafiyar Gaza ta ce adadin Falasdinawan da hare-haren Isra'ila suka hallaka ya haura dubu tara