1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga kan matsalar satar mai a Najeriya

Uwais Abubakar Idris RGB
September 8, 2022

Kungiyar ma’aikatan man fetir da iskar gas sun gudanar da zanga-zangar lumana a Abuja domin nuna damuwarsu kan matsalar satar danyen mai da ake yi a Najeriya.

Symbolbild | Nigeria Gaspipeline
Hoto: Florian Plaucheur/AFP/Getty Images

Kungiyar manyan ma’aikatan man wato PENGASSAN sun gudanar da zanga-zangar lumana a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, yunkuri ne na nuna damuwarsu a kan karuwar satar danyen mai da ake yi a kasar da suka ce, yana neman durkusar da tattalin arzikin Najeriyar da ta dogara a kan arzikin man. 

Ci gaba da ta’azzarar da satar man fetir da ake yi a Najeriya da a yanzu ya wuce hankali da tunanin mahukuntan Najeriyar, wannan ya kai ga tunzura 'ya'yan kungiyar ta manyan ma’aikata da suka kai ga fitowa, don ganin an dauki mataki na hakika a kan lamarin. Ta dai kai ga gwamnatin Najeriyar bayyana cewa kashi casa'in da biyar, na man da ake hakowa a tashar hako mai ta Bonny, sace shi ake yi.

Ta'asar masu fasa bututun mai a jihar BayelsaHoto: Temilade Adelaja/REUTERS

Amma baya ga wannan mummunan dabi’a da ake yi a wasu jihohin da ake hako man Najeriyar, a baiyane take cewa, matsalar ta kai wa kowa a wuya domin duk da amincewar Najeriya da kungiyar kasashe masu arzikin man fetir ta OPEC, na ta hako ganga miliyan 1.8 amma ganga milyan 1,200 take iya samarwa.

Yankin Naija Delta na fama da matsalar malalar maiHoto: Friedrich Stark/imago

Bayanai sun nuna cewa, Najeriyar ta yi asarar dala biliyan goma a watani shida na wannan shekara a fannin satar mai. Akwai sauran kungiyoyi na kwadago da suka shiga zanga-zangar, domin nuna goyon bayansu. Kungiyar mai suna PENGASSAN na zargin cewa akwai hannu na mutanen da dama, musamman al'umman da ke a wuraren da ake hako man fetir, abin da ya kama hanyar durkusar da tattalin arzikin Najeriyar.

Daga batun dama zanga-zangar zuwa ga hedikwatar ‘yan sandan Najeriya da kamfanin albarkatun man a kasar, na nuna cewa, ya fa isa haka a wannan aiki na masu halin bera da ke sace man Najeriya suna durkusar da tattalin arzikin kasar. Yanzu kallo ya koma sama inda ake jiran yadda za ta kaya a kokarin magance wannan matsalar.