1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar zanga-zanga a yankin Hong Kong

Ahmed SalisuDecember 1, 2014

Masu rajin ganin an girka tsarin dimokradiyya a Hong Kong ba tare da katsalandan daga kasar China ba sun yi arangama da jami'an tsaro inda suka tarwatsa su daga wajen da suke.

Polizei geht gewaltsam gegen Demonstranten in Hongkong vor 01.12.2014
Hoto: AFP/Getty Images/D. de la Rey

Da sanyi safiyar Litinin din nan ce jami'an tsaro suka afkawa masu zanga-zangar da ke neman ganin an girka tsarin dimokradiyya a Hon Kong din. 'Yan sandan dai sun farwa mutanen ne a wuraren da suka yi zaman dirshen idan rahotannin da muka samu ke nuna yadda suka lalata tantunan da suka sanya tare da lakadawa wasunsu dukan kawo wuka da ma harba musu hayaki mai sa hawaye.

Baya ga wannan arangama da suka yi, a hannu guda 'yan sanda sun kama masu zanga-zangar kimanin 40 kana sun tura daruruwansu baya da kimanin nisan kimanin mita 200 da inda suka yi zaman dirshen. Wannan hatsaniya ta yau dai ita ce mafi muni da aka gani tun cikin watan Satumban da ya gabata kuma ta yi sanadin rufe wasu ma'aikatun gwamnati da ke yankin.

Masu zanga-zanga sun ce ba su gajiya ba har sai bukata ta biyaHoto: Reuters/Bobby Yip

Wannan ne ma ya sanya masu jagorantar zanga-zangar yin Allah wadai da amfani da karfin da jami'an da suka yi a kansu duk kuwa da cewar ba sa dauke da wani abu da zai cutar da ko da kiyashi. Guda daga cikin masu zanga-zangar ya ce ''bama dauke da makamai amma su sun yi amfani da makaman da ke hannunsu kan mutanenmu, lamarin da ya yi sanadiyar jikkata mutane da dama''.

Yayin da jami'an na tsaro na Hong Kong suka kai ga dakushe kaifin zanga-zangar ta yau musamman ma kokarin da dalibai da sauran jama'a suka na ganin sun hana jami'an gwamnati da ma jagoran yankin zuwa aiki, a hannu guda jagoran masu wannan boren Joshua Wong ya sanar da kudurinsu na fara yajin cin abinci a wani mataki na kara jaddada matsayinsu na fafutukar da suke yi.

Jami'an tsaro sun lashi takobin maido da doka da oda Hong KongHoto: Getty Images/L. Yik Fei

Mr. Wong da sauran abokan burminsu ciki kuwa har da wasu daliban makaranta na sakandare sun ce ba za su jingine wannan yajin nasu na cin abinci ba har sai hakar da suke yi ta kai ga cimma ruwa domin kuwa bukatar da suke da ita ba ta kashin kansu bace, bukata ce ta al'ummar kasar da ma wanda ba a kai ga haifa ba.

To sai dai duk da wannan, shugaban yankin bai nuna kaduwa da halin da ake ciki ba Leung Chun-ying, inda ya ke cewar jami'an tsaro sun yi matukar hakuri da masu bore to amma da ya ke tura ta kai bango yanzu kam za su dauki matakan da suka kamata domin maido da doka da oda.

A wasu kalamai masu kama da martani ga wanda shugaban yankin ya yi, daliban Hong Kong din da sauran masu rajin girka dimokradiyya da kawar da katsalandan din China a tsarin siyasar yankin sun ce ba za su gajiya ba kuma za su yi duk bakin kokarinsu wajen ganin sun gurgunta aikin gwamnati a yankin da ma tsayar da dukannin wata hada-hada chak har sai bukatunsu sun biya.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani