1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Al-Bashir na cikin wadi na tsaka mai wuya

April 9, 2019

A kasar Sudan zanga-zangar nuna kyamar gwamnatin Shugaban Omar Hassan al-Bashir na ci gaba da daukar dumi a ko'ina cikin fadin kasar

Sudanesen protestieren in Dublin
Hoto: picture-alliance/NurPhoto/A. Widak

Tun a ranar Assabar dubun-dubatar masu zanga-zangar ke nuna bukatar murabus din shugaban da ya shafe tsawon shekaru 30 kan madafan iko, tare da nuna fatan ganin sojojin kasar sun shiga an dama da su. To amma sai dai har yanzu masu sharhi na dasa ayar tambaya kan irin goyon bayan da shugaban kasar ta Sudan yake da shi daga wasu kasashen ketare.

A yanzu dai ana iya cewa ta bayyana a fili da Shugaba Omar Hassan al-bashir da ya shafe tsawon shekaru 30 kan madafan iko na iya kwanto  ne kawai da wani bangare na jami'an tsaro na cikin gida, da suka hada da jami'an leken asiri na farin kaya da 'yan sandan kwantar da tarzoma da har yanzu suke makalkalewa ga gwamnatin ta Albashir.

Sai dai bisa rikicin cikin gida da gwamnatin ta Khartum ke fuskanta a yanzu ana iya cewa sojojin kasar sun kama hanyar juyawa Shugaba Albashir din baya duba da yadda har yanzu suka ki cewa Uffan ga masu gudanar da zanga-zangar. Ko da yake duk hakan shugaban na iya kwanto da wasu masu fada aji na kasashen duniya. Michel Galy, wani mai fashin bakin siyasar kasa da kasa ne da ke koyarwa a birnin Paris.

Shugaba Omar al-Bashir na SudanHoto: Reuters/M. Nureldin Abdallah

 

"Ya na iya yin bugun gaba da wasu daidaikun shugabannin kasaszhen kamar na Siriya Bashar al-Assad da alal misali ke fuskantar rangwamen matsin lambar wasu manyan kasashen duniya ciki har na Tarayyar Turai, wanda shi kuma ya gwammaci Albashir din da ya fi sani a hakikance da kuma ke da karfin fada ajin a cikin wasu bangarori na jami'anm tsaron kasar, da masu kaifin kishin addinin islama da baki yan ci rani, maimakon wani wanda bai sani ba bisa bin akida irin ta diflomasiyya, idan har batun tafiyar mulkin na sai mahadi kan turai ta tabbata wadannan batutuwan na daga cikin batutuwan da ake iya tattauanwa kan su, domin samun rigar kariya daga wasu kasashen".

 

To ko wace kasar ce ke iya karbar Shugaba Omar Hassan al-Bashir idan har murabus dinsa daga gadon mulki ta tabbata kamar yadda masu zanga-zangar kasar ke nuna bukata a yanzu? A cewar Roland Marchal, wani kwararre kan harkokin siyasar Sudan Albashir na da tarin mafita:

Dubban masu zanga zangar adawa a SudanHoto: Getty Images/AFP

 

"Ba shakka zango na farko shi ne kasar Saudiyya, na biyu kuwa ana iya hasashen karbarsa a Qatar ko da yake duba da yadda a baya-bayannan tashar gidan talabijin din kasar Aljazeera ke caccakar gwamnatinsa ana iya cewar ba zai samu wata kya-kyawar makoma a can ba, ko da yake komai zai iya faruwa. Ana iya masa ganin wanda zai samu makoma a daular Larabawa, idan kuma hldar da ke tsakaninsa da makocinsa Idriss Daby Itno bata gurbata ba yana iya gangarawa a kasar Chadi ko da ya ke kar a debe shakkun cewar wasu shugabannin na iya sallama takwarorinsu da ba sa kan madafan iko idan har abubuwan suka yi kamari".

 

Duba da kai kalun da rikicin cikin gida da ke addabar gwamnatin ta Sudan a yanzu tuni 'yan adawa suk suka fara nuna zumudin sallamar Shugaba al-Bashir daga kan madafan iko.

Dan shekaru 75, Al-bashir na fuskantar tuhuma ta aikata miyagun laifuka har guda 10 daga kotun kasa da kasa ta ICC ko da ya ke har yanzu suna yiwa juna kallon-kallo tsakanisa da kotun.