1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattalin Arzikin Najeriya ya habaka

December 29, 2020

Duk da jerin matsalolin da suka hada Covid19 da masassara ta tattali na arziki da annobar rashin tsaro, Najeriya ta ciri tutar zama kasa mafi karfin tattalin arziki a Afirka.

Nigeria Symbolbild Korruption
Duk da faduwar darajar Naira da sauran matsaloli, Najeriya na kan gaba a tattalin arzikin AfirkaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Kama daga annobar COVID-19 ya zuwa masassarar tattali na arziki da faduwar farashin man fetur ko bayan batun rashin tsaro dai, shekarar da ke shirin karewa na zaman mai wahala a cikin Tarayyar Najeriyar da 'yan kasarta ke ji a jiki. To sai dai kuma wani rahoto na Asusun Bayar da Lamuni na Duniya IMF, ya nunar da cewa tattalin arzikin kasar na kan gaba a daukacin nahiyar Afirka..

Karin Bayani: Kirismeti cikin larurar corona da rashin kudi

Da girma na tattali na arzikin da ya kai dalar Amirka miliyan dubu 442 dai, Najeriyar ta dara kasashe kamar Afirka ta Kudu da Masar da Moroko. Kasar  dai ce har ila yau tazo  ta 26 a daukacin duniya baki daya ga batu na tattalin arzikin a karon farko da kuma ke nuna irin nasarar jeri na matakan da Abujar ke bi da nufin ceto kanta cikin rukunin masu fama da matsalar tattalin arzikin.
Rahoton da ke zaman na farko a cikin lokacin coronavirus dai, a fada ta Malam Garba Shehu da ke zaman kakakin mahukuntan Najeriyar na nuna irin nasarar matakai na gwamnatin da nufin daukar kasar zuwa tudun mun tsira. To sai dai ko ya shekarar da ke tafen take shiri da ta kaya dai, tun daga makon gobe ne ake sa ran kaddamar da ciniki maras shinge a daukacin kasashe na nahiyar Afirka.

Najeriya na dogaro da arzikin man feturHoto: Construction Photography/Photoshot/picture alliance

Karin Bayani: Matsalar karayar tattalin arziki saboda corona

Kuma Najeriyar na fatan taka rawa mai tasiri a kasuwanci mara shinge na kasashen Afirka, da ke da girman da ya kai dalar Amirka trillion biyu da rabi. Abubakar Ali dai na zaman masani na tattali na arzikin kasar da ke fadin akwai  bukatar taka tsan-tsan ga kasar da karfinta ke  zaman na saye da sayarwa maimakon sarrafa kaya na bukatun al'umma. Duk da yawan kamfanoni a nahiyar dai, ciniki a tsakanin kasashen na Afirka bai kai kaso 20 cikin 100 na daukacin kasuwa ta nahiyar ba. Kuma a fadar Dr. Sani 'Yan Daki da ke  zaman tsohon mataimakin shugaban kungiyar ciniki ta kasar ta NACCIMA, amfanin kasuwar ta bai daya kalilan ne a cikin Najeriyar a halin yanzu.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani