Kasafin kudin Nijar ya gamu da cece-kuce
December 1, 2022Awoyi kimanin 14 ne ‘yan majalisar dokokin kasar suka kwashe suna tafka muhawara kan sabon kasafin kudin wanda ya tashi kudi biliyan dubu uku da miliyan 245 na CFA, wato karin sama da kaso 11 cikin dari ga na shekara ta 2022.
Da kuri'u 135 ne cikin 166 dai majalisar dokokin Nijer din ta amince da dokar kasafin kudin kasar, kuma ‘yan majalisar dokoki 26 na bangaren adawa sun yi watsi da dokar.
Ita ma kungiyar Alternative Espace Citoyen wacce ke sa ido da kuma nazari a kasafin kudin kasa a kowace shekara, ta nuna rashin gamsuwarta da yadda gwamnatin ta tsare kashe kudaden nata a shekarar mai kamawa.
Kusan kaso 50 daga cikin dari na wadannan kudade sama da miliyan dubu uku, gwamnatin ta ce za ta samo su ne daga waje domin kauce wa matsar talaka a cikin gida ta la'akari da tarin matsalolin da dama ke fama da su.