1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Benin ta kama wasu 'yan Jamhuriyar Nijar

June 8, 2024

Hukumomi a Jamhuriyar Benin, sun tabbatar da kama wasu 'yan asalin kasar Nijar su biyar a wata tashar jiragen ruwan kasar, inda suke zargin su da shiga kewayen yankin ba bisa doka ba.

Jami'an tsaro a birnin Cotonou
Jami'an tsaro a birnin CotonouHoto: Abadjaye Justin Sodogandji/AFP/Getty Images

Kamen 'yan Nijar din da aka yi a tashar Seme-Kpodji, ya faru bayan zargin biyu daga cikin su da yi wa sojojin Nijar aiki mai kama da na leken asiri.

Wannan dai ya zo ne yayin da alakar diflomasiyya tsakanin Nijar da Jamhuriyar Benin da ke makwabtaka da juna ke kara tsami.

Bayan juyin mulki na watan Yulin bara a Nijar, kasashe makwabta sun rufe iyakokinsu da kasar, amma daga bisani Benin ta bude tata.

Sai dai hukumomin sojin Nijar sun hana zirga-zirga a tsakaninsu a yanzu ta hanyar ci gaba da garkame iyakar kasashen.