1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Kasar Brazil ta haramta amfani da shafin X

September 1, 2024

Al'umma a kasar Brazil da ma sauran kasashe na ci gaba da tsokaci bayan da kasar ta shiga cikin sahun kasashen da suka haramta amfani da Shafin X wanda aka fi sani da Twitter a baya.

Shugaban Alkalan Kotun Kolin Brazil, Alexandre de Moraes, a yayin zaman yanke hukunci kan dakatar da amfani da X
Shugaban Alkalan Kotun Kolin Brazil, Alexandre de Moraes, a yayin zaman yanke hukunci kan dakatar da amfani da X Hoto: Marcelo Camargo/Agencia Brazil/dpa/picture alliance

Kungiyoyin da ke rajin kare hakkin 'dan Adam na kallon matakin na mahukuntan Brazil din a matsayin wani yunkuri tauye 'yancin fadar albarkacin baki ta kafafen sadarwar zamani.

Karin bayani: Brazil: Kotu ta haramta wa Bolsonaro damar mulki

Toshe shafin a X a kasar ta Brazil dai ya biyo bayan hukuncin da kotun kolin kasar ta zartar, karkashin jagorancin mai shari'a Alexandre de Moraes, bayan da aka bude wasu shafukan X da alkalan kotun suka haramta amfani da su tun da fari.

Karin bayani:Brazil: Lula ya sha alwashin yakar rashawa  

Baya ga Brazil wasu kasashen sun sanyawa al'ummarsu takunkumi na wucin-gadi ko kuma na dindindin wajen amfani da shafin na X, wadannan kasashe sun hada da Masar a lokacin guguwar sauyin kasashen Larabawa a 2011, da kasar Turkiyya a 2014 da kuma 2023 sai kuma kasar Uzbekistan a yayin zaben shugaban kasar a shekara ta 2012. Sauran kasashen sun hadar da Chiana da Turkmenistan da Iran da dai sauransu.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW