1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Canada ta nuna damurwata ga halin kasar Mali

February 14, 2013

Kasar Canada ce ta farko ga sukar lamirin hukumomin kasar Mali bisa ga yadda suke sakaci ga warware rikicin kasar da kan iya rikida zuwa irin na Iraki.

John Baird ministan harakokin wajen CanadaHoto: AP

Ministan harakokin wajen kasar Canada John Baird,ya bayana damuwar kasarsa da ma irin fargaban kasancewar rikicin kasar Mali ya rikida zuwa irin na Afghanistan da Iraki.
Mista Baird ya fadin hakan ne a yayin wata ganawar da yayi da komitin raya kasashen ketare na kasar,inda yace kasar Canada na taka tsantsa a dangane da tura daruruwan dakarunta a kasar Mali kamar yadda wasu kasashen turai suka bukata.
Ministan ya kuma bayana damuwarsa bisa ga abunda ya kira sakacin da hukumomin kasar ta Mali keyi na jiron komai daga kasashen waje. Mista Baird yace akwai abun nuna damuwa ga sha'anin kasar Mali,musamman a kan sahihanci da kuma irin tasirin da horar da dakrun kasar wadanda yace suka kifar da zababen shugaban kasar,kana suka game baki aka lakadawa shugaban kasa dukar tsiya kamun daga bisani kuma su tursasawa praministan rikon kwaryan kasar yin murabus.
Dama dai tun can farko lolakcin da kasar Faransa ta kutsa kai a arewacin Mali,kasar ta Canada ta aika da wani makeken jirgin tattara bayanai domin tallafawa dakarun na Faransa,jirgin da dawainiyarsa zata ci a kalla milyon 16 na kudin Euro kamun karshen yakin da ake saran kammalawa nan da watani buiyu masu zuwa.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Umaru Aliyu