1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Gabon na cikin halin rashin tabbas

Mohammad Nasiru Awal MA
November 16, 2018

Har yanzu babu cikakken bayani game da rashin lafiyar shugaban kasar Gabon Ali Bongo wanda tun a ranar 24 ga watan Oktoban da ya gabata aka kwantar da shi a wani asibitin kasar Saudiyya.

Gabun Still aus einem Video zeigt Gabuns Präsidenten Ali Bongo bei einem Interview in Libreville
Shugaba Ali Bongo na kasar GabonHoto: Reuters/Reuters TV

Tuni kuwa kotun tsarin mulkin kasar ta yi wa kundin tsarin mulkin kwaskwarima don hana samun rudani saboda rashin shugaban kasar na wani gajeren lokaci. Amma, 'yan adawa na cewa kotun ba ta da hurumin daukar wannan mataki.

Jita-jita game da makomar shugaban kasar Gabon Ali Bongo mai shekaru 59, ta yadu kamar wutar daji tun lokacin da aka kwantar da a wani asibiti da ke Riyadh babban birnin kasar Saudiyya a ranar 24 ga watan Oktoba.

Louis Kemayou, dan kamaru masanin kimiyyar siyasa da ya saba karantarwa a kasashen tsakiyar Afirka ciki kuwa har da kasar a Gabon, ya ce babu tabbacin cewa a cikin iyalin Bongo za a samu wanda zai gaje shi kasancewar babu ko daya daga cikin 'ya'yansa da suka taba rike manyan mukaman gwamnati. Sannan kusoshin jam'iyyar PDG mai mulki da wadanda suka juya mata baya ciki har da madugun adawa Jean Ping, ba su yarda wani dangin Bongon ya sake zama shugaban kasa ba, haka ma al'ummar kasar.  A ganin masanin Ali Bongo zai zama danginsu na karshe da zai yi mulki idan karshenshi ya zo.

Hoto: Getty Images/AFP/M. Longari

An dai taba fuskantar juyin mulkin soja a kasar Gabon a shekarar 1964. Sai dai ana kawar da faruwar hakan a wannan karon duk da damar da sojoji ke da shi na hambarar da gwamnatin Ali Bongo. Dalili kuwa shi ne dan uwan shugaban kasar ne ka jagorantar rundunar da ke kare lafiyar shugaban.

 

Wilson-André Ndombet masanin kimiyyar siyasa a Gabon ya ce juyin mulki zai mayar da hannun agogo baya a fannin dimukuradiyya.

"Juyin mulki zai gurganta duk harkokin mulki, zai share duk wani ci gaban dimukuradiyya da kasarmu ta samu. Idan sojoji suka karbi mulki, ba a san yawan lokacin da za su shafe kafin su yarda a yi zabe ba, duk da cewa an san dimukuradiyyar na tafiyar hawainiya. Amma tabbas kowa na cikin fargaba a Gabon game da abin da ke faruwa musamman ma talakawa"