1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

kasar Gini na dakon sakamakon zaɓe

October 1, 2013

Alamu sun nuna cewar babu jam'iyyar da za ta samu rinjaye a zaben 'yan majalisa na Gini, duk da kallon hadarin kaji da 'yan siyasa ke yi wa junansu lokacin da ake kirga kuri'u..

A woman casts her ballot at a polling station in Guinea's capital Conakry September 28, 2013. Guineans voted on Saturday in a parliamentary election to complete its transition to democracy after a 2008 military coup and end decades of political instability. REUTERS/Saliou Samb (GUINEA - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Hoto: Reuters

Hukumomi a ƙasar Gini sun yi gargaɗin ɗaukar matakan hukunta waɗanda ke neman haifar da ruɗani wajen bayyana sakamakon boge, game da babban zaɓen majalisar dokokin kasar. Wannan yana zuwa ne a dai dai lokacin da al'ummar ƙasar ke zaman jiran cikakken sakamakon karshe na zaben 28 ga watan satumban da aka gudanar a ƙasar.

Magoya bayan dukkanin ɓangarori ne suka ɗauka kan titunan ƙasar suna bayyana farin cikin samun nasarar zaɓen tun gabanin hukumomi su kammala kiɗayar ƙuri'u bayan gama tantancesu. matakin da hukumomin ƙasar ke ganin ya isa haifar da ruɗani ga makomar kasar, da ake yi wa fatan bin sahun maƙociyar ta Mali, da ta kammala na ta cikin kwanciyar hankali da lumana

Zaɓen na ƙasar Guinea kamar yadda aka saba gani a sassan nahiyar Afirka yana da na sa matsaloli, da suka danganci rashin daidaituwar mizanin masu ƙuri'a a mazaɓu bisa tsarin da dokar ƙasa ta tanada, wannan ya haifar da sauyawa wasu mazauna unguwanni guraren kaɗa ƙuri'u. Waɗannan dai kusan su ne matsaloli da masu sanya idanu ke ganin ya kamata a sanya gaba domin kawo gyara a zaɓuka nan gaba

Rigingimun 'yan adawa kafin zaɓeHoto: picture-alliance/AP

Landana Kouyate shine shugaban babbar jam'iyyar hamayya ta PEDN, ko waɗanne abubuwa su ke ganin sun saɓawa tunaninsu game da zaɓen:

"Wasu daga cikin wakilan mu sun bayyana mana wasu matsaloli da masu daukar hankali, kuma tuni muka rigaya muka aikawa kungiyoyin kasa da kasa dake sanya ido a wannan zabe nan take, fatan mu dai wannan yanayi na lumana zai dore da adalci".

Martanin ƙungiyoyi masu sanya ido

Tuni ƙungiyoyin sanya ido ke cigabada daukar dukkanin matsaloli dasuke ganin sun taka rawa wajen haifar d atarnaki, musamman a wanan lokaci da bangarorin yan takara ke haifar da rudani a zukatan al umma ta hanyar aika sakonnin boge game da nasara lashe zabe, duk kuwa da gazawar hukumar zaben kasar ta wasu bangarori da masu sanya idon ke ganin zai haifar da rudani.

A cewar hukumar zaben kasar CENI, bata fuskantar wata matsala inji baturen zaɓe Sekou Kourouma

"Muna aikin tantancewa kuru'un da aka kada ne gaban dukkanin wakilan jam'iyu masu mulki dana adawa, a takaice dai bamu fuskanci wata matsala game da hakan ba."

Fargabar masu zaɓe

Tuni masu sanya idanu na Ƙungiyar Tarayyar Turai suka fara bayyana damuwa game da sakamakon da ka iya biyo bayan bayyana sakamakon zaɓen ta Majalisar Dokoki, baya ga matsaloli da suka shafi gudanar wa shi kansa jaddawalin dake ɗauke da sunayen masu zabe bai samu wani gyaran fuska dai dai da yanayin da ake ciki a kasar ba, hakan kuwa ya shafi halarcin zaben kansa.

Wasu sunayen sun ɓace yayin da wasu suka bayyana fiye da sau guda, alamu dai na nuni da cewa babu wata jam'iyya da za ta samu rinjaye cikin zauren majalisar, hakan kuwa zai bayar da damar kawance tsakanin jam'iyyun da wakilan su suka samu shiga ƙunshin sabuwar majalisar mai wakilai 114.

Mawallafi: Garzali Yakubu
Edita: Pinaɗo Abdu Waba

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW

Karin labarai daga DW