1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Holland ta aika da makaman kariya ga Turkiya

January 7, 2013

Tun bayan barkewar rikicin Siriya,hukumomi a Turkiya ke nuna fargabansu a dangane da makamai masu lizame da ke fadawa a kasarta daga Siriya.

Hoto: Deutsche Bundeswehr/Getty Images

Goman motoci ne dauke da karafunan hada makaman kariya suka tashi daga kasar Holland ya zuwaTurkiya a wannan Litanin . Dama dai tun can farko kasar ta Holland ta yi arkaawarin aikawa Turkiya wasu makaman kariya daga barazanar faduwar makamai masu nizamae na kasar Siriya. Rahotani daga kamfanin dillancin labaran Reutres,sun bayana cewar a kalla motacin sulke na sojin kasar Holland 160 ne ke dauke da kayan da za a hadawa domin kafa kariya ga kasar ta Turkiya da ta bukaci kasashen kungiyar NATO da su kare ta daga barazanar faduwar makaman da ake harbawa daga makwabciyarta Siriya. A lokacin da ya kewa manema labarai magana.laftana kanar Marcel Buis na rundunar tsaron Holland,ya ce Siriya nada makan masu cin dogo da gajeren zango wadanda kuma ke iya kaiwa ga wasu mahimman biranen Turkiyar,don haka wajibi ne ga NATO da ta taimaka wa daya daga cikin mambobinta.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Mahammad Nasiru Awal