1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Iran ta daure wani jami'in nukiliya

Mouhamadou Awal Balarabe
October 8, 2017

Hukuncin shekaru biyar ne kotun Teheran ta yanke wa wani jami'in Kanada Abdolrasoul Dorri Esfahani da aka dama da shi a yarjejeniyar nukiliyar Iran bisa laifin leken asiri.

Justiz Justizchef Amoli Larijani Iran
Hoto: Fars

Hukumomin Iran sun sanar da yanke hukuncin shekaru biyar a gidan yari ga  wani dan Kanada da aka dama da shi a shawarwari kan yarjejeniyar nukiliyar Iran da aka cimma a watan Yulin 2015. Kakakin ma'aikatar shari'a ya nunar da cewar Abdolrasoul Dorri Esfahani, wanda dan asalin kasar ta Iran ne yana daga cikin gungun mutane, da aka samu da laifin yin leken asiri da kuma samar da bayanai ga 'yan kasashen waje. jami'in ya kara da cewa hukunci na kololuwa ne saboda haka Mista Dori ba zai iya daukaka kara ba.A baya dai Ministan da ke kula da harkokin leken asirin IranMahmud Alavi ya yi watsi da zargin da aka yi a watan Oktoba 2016, amma kotun ta ci gaba da shari'ar har ta kai ga yanke hukunci.

Idan za a iya tunawa dai manyan kasashen dunyia shida ciki har da Jamus sun yi tsayuwar daka wajen ganin an sanya hannu kan yarjejeniyar nukiliya da Iran don hanata kera makamin kare dangi. Sai dai kuma shugaban Amirka Donald Trump ya yi barazanar janye kasarsa daga yarjejeniyar, da ta sanya aka dakatar da takunkumin tattalin arzikin da aka kakaba wa Iran.