kasar Jordan ta haramta ayyukan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi
April 23, 2025
Masarautar Jordan ta haramta duk wasu ayyuka na kungiyar 'Yan Uwa Musulmi tare da rufe ofisoshinta a fadin kasar, bisa zarginta da yunkurin kawo cikas ga zaman lafiya ciki har da kerawa da kuma adana rokoki da bama-bamai. Wannan mataki ya zo ne kwanaki kalilan bayan da mahukunta suka kama mutane 16 da suka hada da 'yan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi, wadanda ake zargi da neman kassara tsaron kasa da haddasa hargitsi da kuma yin zagon kasa ga kasar Jordan. Sai dai kungiyar ta musanta zargin da ake mata, tana mai nuni da cewar daidaikun mutune ke yin gaban kansu domin nuna goyon bayan halin da Falasdinawa ke ciki.
A baya dai, mahukuntan Jordan sun rufe ido kan ayyukantan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi duk da hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke a 2020 na rusa kungiyar a fadin kasar. Hasali ma dai, bangaren siyasa na kungiyar ya zama jam'iyya mafi girma a majalisar dokokin Jordan, inda ta lashe kujeru 31 daga cikin 138 a zaben da aka yi a watan Satumban bara.