1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Kenya ta nuna bacin ranta ga kasashen G8

January 11, 2006

Mahukuntan kasar Kenya sun bayyana rashin jin dadin su ga kasashen G8 ,a game da kin saka sunan kasar a cikin jerin kasashen da za´a yafewa bashi.

A cewar ministan kudi na kasar, wato David Mwiraria da alama kasashen na G8 sun yi hakan ne da gangan don ladaftar dasu a game

da kyakkyawan ci gaba da kasar ta samu a fannin tattalin arziki.

A cewar ministan dinbim bashin da kasashen na G8 suke bin kasar ta kenya na daya daga cikin matsalolin kasar na rashin samun ingantaccen tattalin arziki a kasar.

A karshe ministan ya tabbatar da cewa, wasu daga cikin kasashen da aka tsara yiwa yafiyar , kasar ta Kenya tafi su matsaloli dake da nasaba da tattalin arziki.

A dai shekarar data gabata ne, kasashe masu arzikin masana´antu na duniya da aka fi sani da suna G8 a turance suka bayar da sanarwar yafewa wasu matalautan kasashe dimbin bashin da suke bin su.