Kasar Libiya ta fada cikin rikicin siyasa
January 22, 2012Mataimakin shugaban gwamnatin rikon kwarya a Libiya Abdul Hafiz Ghoga ya yi murabus. Ghoga yace ya ajiye aikinsa ne bisa jerin zanga-zanga da aka yi ta gudanarwa a kasar, abinda kuma kamar yadda ya kwatata da cewa ba zai yi wa kasar alheri ba. Boren da ake yi dai ya girgiza gwamnatin rikon kwarya, abinda ya sa ake gudun rugujewar al'amura a kasar, wanda ke farfadowa tun bayan farmakin da yakin basa da kuma hare-haren jiragen yaki na kasashen kungiyar tsaro ta NATO, wadanda suka kai ga kisa da kuma kifar da gwamnatin Muammar Gaddafi. A yammacin jiya matasa da suka fusata a birnin Benghazi sun kutsa kai cikin ginin gwamnati a dai-dai lokacin da babban jami'i mafi girma a birnin ke cikin ofishin, inda suke bukatar sai gwamnatin rikon kwaryar wanda aka sani da NTC ta yi murabus.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu