Kasar Nijar na kan hanyar samun jirgin kasa
April 10, 2014 An gudanar da wadannan shagulgulla ne a karkashin jagorancin shugabannin kasashe uku da abun ya shafa, da suka hada da shugaban kasar Benin, da na Togo da kuma mai masaukin baki Shugaba Issoufou Mahamadou na Jamhuriyar Nijar. Sai dai kasashe kamar su Najeriya, Burkina Faso, da ma Cote d'Ivoire da su ma ke cikin wannan tsari, sun aike da ministocinsu na sufuri wajan wannan buki.
Hanyar dai ta jirgin kasa ko layin dogo, mai nisan kilomita dubu, za ta taso ne daga Jamhuriyar Benin, ya zuwa birnin Yamai, inda aka bada kwangilar shimfida ta ga wani kamfani na kasar Faransa da ya yi fice wajen shimfida hanyar jirgin kasa da ake kira Bolloré, kuma aikin zai ci akalla kudi tsaba CFA miliyan dubu dari bakwai.
Babbar rana ga kasashen yammacin Afirka
Da yake bayani kan wannan batu, shugaban Nijar Alhaji Issoufou Mahamadou ya ce:
"Wannan babbar rana ce ga al'ummar Nijar, domin shekaru wajen 80 ake jiran wannan hanya ta layin dogo, sai gashi a yau an fara aikin ta da yardar Allah.W
Ana gani dai, idan wannan hanya ta kammala, za a samu sauki sosai wajen zirga-zirgar harkokin kasuwanci da ma na fasinja a tsakanin kasashen, wanda ake ganin ba karamin ci-gaba ba ne ga rayuwar al'ummomin kasashen na yammacin Afirka. Alhaji Sidi Moussa Mohamed, shugaban cibiyar kasuwancin Nijar ya yi bayani, inda yake cewa:
"Musamman talakawa za su ci moriyar wannan tsari, kuma duk wata matsalar fatauci ta dalilin nisantar Teku za ta yi sauki, sannan kuma ana sa ran a samu saukin farashin kayayyaki idan har kudadan sufuri suka ragu, abin da zai samar da walwala da ma bunkasar tattalin arzikin al'umma da ma kasar baki daya."
Shugaban na cibiyar kasuwancin ta Nijar, ya kara da cewa:
"Duk da haka, idan ma wannan jirgin na kasa ya samu, to ba za mu kauda safarar motoci ba, za mu ci gaba da daukan fasinja da ma kayayyaki kamar yadda muka saba."
Rayuwar talakawa za ta inganta
Daga nasu bangare su ma talakawa sun nuna murnarsu a fili kan wannan batu, inda suka yi fatan rayuwa za ta canza, farashi kayayyakin abinci zai yi sauki, sannan a fuskar kasashen Afirka ta yamma, ana ganin za a cimma buri na samun kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashen.
Tuni dai aka shimfida hanyar a birnin Yamai mai kimanin tsawon mita 200, inda aka kawo kan jirgin da wasu taragogi, kuma shugabannin uku tare da manyan mutanen da suka halarci bukin, suka shiga aka yi 'yar tafiya a matsayin gwaji.
Mawallafi : Mahamane Kanta / Salisou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal