1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Ana yin zaman makoki a Ostiriya

Abdourahamane Hassane
June 11, 2025

Kasar Ostiriya na gudanar da zaman makoki a yau Laraba, kwana guda bayan da wani tsohon dalibi ya harbe mutane goma a wata makaranta a Graz kafin ya kashe kansa.

Hoto: Darko Bandic/AP

A gaban makarantur sakandare, a tsakiyar gari, da majami'u,  mazauna garin sun kunna kyandir tare da shimfida furanni don karrama wadanda suka mutu, wadanda galibinsu matasa ne. Wanda ya kai harin ya yi amfani da babbar bindiga wadda yake da lasisin mallakarta.

Ya yi karatu a  wannan makarantar sakandire da ke daukar nauyin matasa kusan 400 masu shekaru 14 zuwa 18, amma bai kammala karatunsa ba.